PDP v APC: ‘Dan Takara Ya Tafi Kotun Karar Zabe da Takardu 8000 Su Zama Hujjoji

PDP v APC: ‘Dan Takara Ya Tafi Kotun Karar Zabe da Takardu 8000 Su Zama Hujjoji

  • Dapo Abiodun ya yi galaba a zaben Gwamnan Jihar Ogun da aka yi a watan Maris, amma ana kotu
  • ‘Dan takaran PDP ya na kalubalantar nasarar da Hukumar INEC ta ba Abiodun da Jam’iyyar APC
  • Goddy Uche (SAN) ya sheka kotu da wasu rahoton na’urar BVAS da takardun INEC a matsayin hujjoji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - ‘Dan takaran PDP a zaben Gwamnan Ogun da ya wuce, Ladi Adebutu ya tafi kotu da takardu 8, 000 a matsayin wadanda za su zama hujjojinsa.

The Guardian ta ce wadannan takardu za su zama shaida a kotun da ke sauraron karar zaben da Ladi Adebutu yake ja da Gwamna Dapo Abiodun.

George Uche (SAN) wanda shi ne babban lauyan ‘dan takaran, a kotun zaben ya gabatar da takardu a jakar nan da aka fi sani da “Ghana-must-go”

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

PDP a Ogun
Yakin zaben PDP a Ogun Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Hujjojin da lauyan PDP ya tanada

Daga cikin takardun da Lauyan ya kafa hujja da su akwai bayanan BVAS, rajistar masu zabe, sakamakon zaben jihar Ogun daga IREV da wasu fam.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce George Uche ya dumfari kotun sauraron karar dauke da takardar korafi mai shafuka 98, ya na kalubalantar Gwamna, APC da hukumar INEC.

Daga nan lauyan ya bukaci a ba shi dama ya fara jero hujjojinsa a shari’ar zaben.

Lauyoyin Gwamna da APC ba su yarda ba

Peter Olatunbora a matsayinsa na lauyan mai kare hukumar zabe bai amince da wannan magana ba, ya bukaci mai karar ya fara nuna hujjojin na sa.

Shi ma lauyan da ya tsayawa Gwamnan, Kehinde Ogunwunmiju ya zargi Uche da sabawa ka’idar kotun karar zabe, wannan shi ne ra’ayin Lauyan APC.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

Premium Times ta ce Kunle Kalejaye (SAN) ya ce lauyan ‘dan takaran PDP ya na kokarin yi wa kotu dabara ne wajen gabatar da hujjojinsa a gabanta.

Kotu za ta cigaba da zama a gobe

A dalilin haka, shugaban da ke sauraron karar zaben Gwamnan, Hamidu Kunazaya ya ba Uche kwanaki biyu domin ya nuna duk hujjojin da yake da su.

Daily Trust ta ce Alkalai uku a karkashin jagorancin Hamidu Kunaza, su ke sauraron wannan kara mai lamba EPT/OG/GOV/03/2023 a kotun na Abeokuta.

Kotun korafin zaben ta ce za a cigaba da sauraron shari’ar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.

Lauyoyin NBA vs Tinubu

A rahotonmu, kun ji cewa wasu Lauyoyin kasar nan sun rantse za su kafar wando daya da gwamnatin Bola Tinubu a kotu saboda harajin POC da aka kawo.

Kungiyar NBA-SPIDEL ba ta goyon bayan a wajabtawa masu abin hawa biyan karin haraji. Gwamnatin tarayya ta kirkiro N1000 da za a rika biya duk shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng