Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da sabbin jagororin majalisar a zaman yau Talata, 4 ga watan Yuli, 2023
- Akpabio ya bayyana waɗanda suka samu nasarar zama shugaban masu rinjaye, marasa rinjaye, mai ladabtarwa da mataimakansu
- Bamidele, Dave Umahi, da Sanata Ali Ndume na cikin sabbin jagororin da aka ji Akpabio ya ambaci sunayensu a zaman Sanatoci
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da waɗanda suka samu nasarar zama jagororin majalisar dattawa ta 10.
Channels tv ta tattaro cewa Sanata Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi sabbin shugabannin ne ta hanyar maslaha.
Jagororin bangaren masu rinjaye
Sabbin jagororin majalisar sun haɗa da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Dave Umahi daga Ebonyi a matsayin mataimakinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya zama babban mai ladaftarwa na majalisa yayin da Sanata Lola Ashiru, ya samu nasarar zama mataimakinsa.
Sabbin jagororin majalisar dattawa daga ɓangaren marasa rinjaye
A ɗaya bangaren kuma Sanata Akpabio ya bayyana sabbin shugabanni daga ɓangaren marasa rinjaye.
Sun ƙunshi Sanata Simon Davou (Filato ta arewa – PDP) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye yayin da Oyewunmi Olarere (Osun ta yamma – PDP) ya zama mataimakinsa.
Sauran sun haɗa da Sanata Darlington Nwokeocha mai wakiltar jihar Abia ta tsakiya a inuwar LP a matsayin mai ladaftarwan marasa rinjaye da kuma Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya) a matsayin mataimakinsa.
Idan baku manta ba 'yan takarar da jam'iyyar APC ta marawa baya ne suka samu nasarar zama shugabannin majalisar tarayya ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni, 2023.
Godswill Akpabio ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa yayin da Honorabul Tajudeen Abbas ya zama sabon kakakin majalisar wakilan tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Sani Yerima
A wani labarin na daban kuma bayam ganawa da shugaban kasa, Sanata Yerima ya ce shugaba Tinubu ya ɗora masa alhakin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara.
Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta yi wa katutu a shiyyar Arewa maso Yamma yayin da 'yan bindigan jeji da masu garkuwa suka hana mutane rawar gaban hantsi.
Asali: Legit.ng