Ministocin Tinubu: Jigon APC Jack-Rich Ya Musanta Zargin Bai Wa Gbajabiamila Cin Hanci Don A Bashi Mukami

Ministocin Tinubu: Jigon APC Jack-Rich Ya Musanta Zargin Bai Wa Gbajabiamila Cin Hanci Don A Bashi Mukami

  • Masu yaɗa labaran jigo a jam'iyyar APC, Tein Jack-Rich, sun yi watsi da yunkurin alaƙantasa da bayar da cin hanci
  • Masu taimakawa dan siyasar kuma ɗan kasuwa a kafafen yaɗa labarai, sun ce zargin da ake yi wa ubangidan nasu ba shi da tushe balle makama
  • Sun kuma bayyana cewa masu yaɗa wannan jita-jita sun firgita ne da yadda Jack-Rich ke samun ɗaukaka a siyasar kasar nan

Birnin Tarayya, Abuja - Tein Jack-Rich, ɗan takarar shugabancin ƙasa a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC, ya ƙaryata zargin da ake masa na bayar da cin hanci don a sanya shi cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu.

Hakan na zuwa ne bayan da wani mai suna Jackson Ude, ya bayyana cewa Jack-Rich ya bai wa Gbajabiamila miliyan 500 don a sanya sunansa cikin ministoci, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Na Ke Ware Wa Jami'an Kan Hanya Yayin Jigilar Shanu Daga Arewa Zuwa Kudu, In Ji Isiaka

Jack-Rich ya musanta zargin ba da cin hanci
Tein Jack-Rich ya ce bai ba Gbajabiamila cin hanci ba. hoto: @jackrichtein, @femigbaja
Asali: Twitter

Baya ga zargin bayar da cin hanci, jaridar The Punch ta wallafa cewa Jackson ya zargi Mista Jack-Rich da barin matarsa Elizabeth, yin wasu abubuwa da basu dace ba.

A wata sanarwa ta martani da masu kula da shafukansa suka aikawa Legit.ng a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, jigon na jam’iyyar APC ya bayyana cewa zargin bayar da cin hancin da ake yi masa bashi da tushe balle makama, kuma wasu mutane ne suka dauki nauyinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu 'yan siyasa ne ke ƙoƙarin ɓata sunan jigon na APC da na Gbajabiamila

Sanarwar ta bayyana cewa wasu masu neman gindin zama a siyasa ne ke ta ƙoƙarin ƙirƙiro labarai marasa tushe gami da jinginasu ga ubangidansu.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun yi matukar kaɗuwa, cewa a yunƙurinsu na ɓata sunan Mista Jack-Rich da iyalinsa,"

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

“Wasu daga irin waɗannan ‘yan siyasan za su iya yin kowane irin kalamai ne waɗanda ba wai iya kan Jack za su tsaya ba, za su kai har ga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, ta yadda za suyi hakan don su ɓata masa suna, wanda daga ƙarshe har abin ya shafi shugaban ƙasa.”

Sanarwar ta yi nuni da cewa, wannan ba shi ne karo na farko da mawallafin irin waɗannan zarge-zargen ya yi yunƙurin ɓata Mista Jack-Rich ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Haka zalika, a shekarar 2021, Mista Jackson Ude, shi ne ya fitar da wani rubutu, inda ya yi zargin cewa Mista Tein Jack-Rich na da hannu wajen badaƙalar kuɗaɗen haram ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, saboda wanda ya turo Jackson Ude yana kallon Mista Jack-Rich a matsayin ɗan siyasar da ya shigo domin yin kyawawan abubuwa ga ƙasa."
"Har ya zuwa yau, duka zarge-zargen ba su da wata makama, kuma har yanzu ba a iya gano shi Jackson Ude da iyayen gidan nasa ba."

Kara karanta wannan

Dan Majalisa Mafi Karancin Shekaru: Yadda Rasuwar Yayana Ya Yi Sanadin Shiga Ta Siyasa

Jack-Rich ya cancanci kowane irin muƙami, in ji mai taimaka masa a kafofin yaɗa labarai

Masu taimaka masa sun bayyana cewa a matsayinsa na babban mai ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, Jack-Rich yana da dukkan abin da ya dace wajen sanya shi a kowane ofishi ne Shugaba Tinubu ya ga ya dace, kuma ba ya bukatar bayar da cin hanci ga kowa.

An kuma bayyana Jack-Rich a matsayin mutum mai biyayya kuma cikakken ɗan jam’iyya wanda a tarihi bai taɓa zama ɗan wata jam’iyyar siyasa in ba APC ba.

Lokacin da ake tsammanin zuwan ministocin Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo wani rahoto da yake magana a kan lokacin da Tinubu zai miƙa sunayen mutanen da yake so ya naɗa ministoci ga Majalisar Dattawa.

Ana sa ran cewa, Shugaba Tinubu zai miƙa sunayen ministoci nasa ne a kowane lokaci bayan 4 ga watan Yuli mai kamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel