Hajj 2023: Gwamna Bala Mohammed Na Jihar Bauchi Ya Jagoranci Mahajjata Musulmi Sallah A Makka

Hajj 2023: Gwamna Bala Mohammed Na Jihar Bauchi Ya Jagoranci Mahajjata Musulmi Sallah A Makka

  • A aikin Hajji bana da ake yi a birnin Makkah na kasar Saudiyya, an hangi wani gwamnan Najeriya da ya jagoranci wasu daga cikin mahajjata sallah
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya jagoranci taron addu'a a ranar Arfa, wato ranar Talata 27 ga watan Yuni
  • An hango jigon na jam'iyyar PDP a gaban wasu tarin alhazai a bayansa da ya jagoranta sallah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Makkah, Saudi Arabiya – Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi, ya bayyana cewa ya jagoranci tawagar alhazai a aikin Hajjin bana a Makka da ke kasar Saudiyya.

Legit.ng ta tabbatar da hakan a wani hoto da gwamna Bala Mohammed ya dora a shafinsa na Fesbuk, a ranar Talata, 27 ga watan Yuni.

Sanata Bala Mohammed a Makkah
Sanata Bala Mohammed ya jagoranci Alhazai sallah a Makkah. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

A cikin sakonsa da ya rubuta cikin harshen Larabci a shafinsa na Fesbuk, ya yabi Allah ta hanyar girmama Shi da kuma daukaka girmansa gami da yin tasbihi a gare Shi.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: CAN Ta Taya Musulmai Murnar Bikin Layya, Ta Nemi A Yi Addu'o'i Don Zaman Lafiya

Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Fesbuk:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Allah mai girma, Allah mai girma, Allah mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya face Allah, Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya, Shi ne mafi girma, kuma godiya ta tabbata a gare Shi, Shi rayayye ne, kuma Shi ne Mai ikon kan komai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah."

Gwamna Bala ya yi addu'ar zaman lafiya ga Najeriya

Jigon na jam’iyyar PDP ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya, tare da rokon Allah ya jikan Najeriya da al’ummarta da fatan Allah ya bai wa al’ummar kasar kwanciyar hankali da nutsuwa.

Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’ar samun rayuwa mai albarka da shugabanci na gari da zai ciyar da Nijeriya gaba a yayin gudanar da aikin Hajjin na bana.

Kara karanta wannan

Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah

A kalaman gwamna Bala Mohammed:

“Ya ku ‘yan uwa Musulmi, mu yi amfani da wannan rana wajen addu’ar Allah ya ba mu rayuwa mai albarka, arziki mai albarka, ‘ya’ya masu albarka, da shugabanci nagari wanda zai gyara kasarmu."
“A matsayinmu na shugabanni, ya Allah, ka yi riko da hannayenmu, kada ka bar mu da iyawarmu, ka sanya tsoronka a cikin zukatanmu, kada ka bar mu mu bi son zukatanmu. Ya Allah ka karbi ibadunmu da addu'o'inmu."

Alhazan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar abinci

a baya, Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan Alhazan jihar Osun da suka gudanar da wata zanga-zanga a kasa mai tsarki.

Alhazan dai sun gudanar da zanga-zangar ne sakamakon rashin ingancin abincin da suk ce hukumar jin dadin Alhazan jihar Osun din ke ba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng