Hadimin Wike Ya Dauki Zafi, Ya Fadi Abin da Ya Jawo Atiku Ya Fadi Zaben 2023
- Maganganun da su ka fito daga bakin Phrank Shaibu, sun jawo Marshal Obuzor ya maida martani
- Tsohon Hadimin na Nyesom Wike ya ba tsohon Gwamnan kariya daga ‘dan takaran shugaban kasar
- Obuzor ya yi kaca-kaca da Atiku Abubakar, ya ce ta kare masa a siyasa shiyasa yake faman babatu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - A wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Marshal Obuzor ya ce babu abin da ya hana Atiku Abubakar samun mulkin kasar nan illa girman kai a siyasa.
Tsohon hadimin na Nyesom Wike ya caccaki ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP, ya ce akwai bukatar a tausaya masa, rahoton ya zo a Vanguard.
A cewar Marshal Obuzor, takaici ya lullube Atiku Abubakar saboda abin da ya faru a zabe.
Wannan duk ya zo ne a cikin raddin da Obuzor ya yi wa a Phrank Shaibu wanda ya na daya daga cikin masu taimakawa Atiku Abubakar wajen harkar sadarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Phrank Shaibu ya tsokano Wike
Phrank Shaibu ya fito ya na maidawa Nyesom Wike martani bayan ya yi bayanin yadda ya yi fama da cutar koda da hanta a sakamakon wani tarkon guba.
Hadimin tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce babu wanda ya yi yunkurin kashe tsohon Gwamnan da guba, a cewarsa giya ce kurum ke yi masa illa.
A jiya The Cable ta rahoto Obuzor ya ce jawabin da aka fitar a madadin ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna rashin zurfin tunani da takaicin da ke damunsa.
Mai ba tsohon Gwamnan shawaran ya kare mai gidansa, yake cewa binciken masana ya tabbatar da guba tayi wa Wike illa, ba giyar da ake ikirari ba.
Raddin Marshal Obuzor ga Atiku
"A karshe mutum ba zai zargi Atiku da nuna irin wannan takaici ba domin shekaru 30 kenan ya na takara a kowane zabe tun 1993, amma ba a zaben shi.
Ganin ana neman daina damawa da shi, a daina maganarsa a siyasa, zai yi ritaya ba tare da nasara a zabe ba, Atiku ya fusata, ya zama wani abin tausayi.
Za a fahimci silar takaicinsa kuma a zahiri yake ta kare masa a siyasa, ko Atiku ya kalli madubi, zai tausayawa kansa kan yadda ya barar da damarsa na mulki.
- Marshal Obuzor
Zaben Shugabannnin Majalisa
Rahoto ya zo cewa Nyesom Wike ya yi kus-kus da su Godswill Akpabio da Jibrin Barau a kan zaben shugabannin majalisa, ya na mai yakar jam'iyyarsa.
Wike ya na tare da Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi a G5 kuma ba su goyon bayan ‘yan takarar Atiku Abubakar da PDP.
Asali: Legit.ng