Makusancin Atiku Abubakar, Idi Amin, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Abuja
- Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Maiha da ya gabata a Adamawa, Idi Amin, ya rasu a birnin tarayya Abuja
- Marigayin ya yi kaurin suna a siyasa saboda salonsa da yawan ba da nishaɗi kuma masoyin Atiku Abubakar ne
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, na jihar Adamawa ya miƙa sakon ta'aziyya tare da addu'ar Allah ya gafarta masa
FCT Abuja - Mamban kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Idirissu Amin, wanda aka fi sani da Idi Amin, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Idi Amin, makusanci kuma ɗan a mutun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya rasu ne a birnin tarayya Abuja.
Wata majiya daga cikin iyalan gidansa ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Bayanai sun nuna cewa marigayi Idi Amin, ya riƙe kujerar shugaban karamar hukumar Maiha a jihar Adamawa, shiyyar Arewa Maso Gabas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan Idi Amin, ɗan siyasa ne mara tsoro kuma mai girman jiki irin na tsohon shugaban ƙasar Uganda, ya yi kaurin suna a lungu da saƙon Adamawa saboda ɗabi'arsa ta yawan bada nishaɗi.
Gwamna Fintiri ya aike da saƙon ta'aziyya da Addu'a
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayin a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, ya fitar.
Ya ayyana marigayi Amin a matsayin ɗan siyasa mara tsoro, wanda ya ba da gudummuwa mai matuƙar yawa a ƙasar nan, Sahara Reporters ta ruwaito.
Sanarwan ta ce:
"Ina miƙa akon ta'aziyya ga iyalansa yayin da muke jimamin rasuwar babban ɗan siyasa mara tsoro a kan duk a abinda ya tsayu a kai. Muna takaicin rashinsa a daidai lokacin da jiharmu ke buƙatar Honorabul Idi Amin."
"Ina fatan Allah ya bai wa iyalansa karfin zuciyar jure wannan babban rashi kuma Allah ya gafarta masa ya sa shi a cikin gidan Aljannatul Furdausi."
Bayan haka gwamna ya yi ta'aziyya ga ɗaukacin mutanen ƙaramar hukumar Maiha da jihar Adamawa baki ɗaya, inda ya ƙara da Addu'ar Allah ya karɓi bakuncinsa ya sanya shi a gidan Aljanna.
Mutumin kirki ne ga son kafa matasa
Wata 'yar jihar Adamawa, Maryama Haruna Ch, ta tabbatar wa wakilin Legit.ng Hausa cewa marigayi idi Amin mutumin kirki ne kuma mai taimaka wa matasa don su tsaya da kafafuwansu.
A cewarta, samun mutum irin sai an tona domin ko ba a ƙaramar hukumarsa kake ba zaka amfana da irin tallafi da kokarin gina jama'a musamman matasa da yake yi.
A kalamanta, Maryama ta shaida wa wakilinmu cewa:
"Mutumin kirki ne na mutane, ba shi da hassada ko ƙyashi ga son addini da riƙo da shi. Mutum ne mai son yaga kullum matasa sun ci gaba kowanne ya zama yana dogaro da kansa."
"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000
"Idan har za a yi alfahari da wasu 'yan siyasa a jihar Adamawa to gaskiya idi Amin yana ciki. Bani da wata dangantaka da shi amma ayyukansa na Alheri suna zagaya ko ina."
Daga ƙarshe, ta yi fatan halayensa na kwarai su bi shi zuwa ƙabarinsa kuma ta yi Addu'ar Allah ya saka masa da mafificin sakamako.
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Alhazan Najeriya 2 Suka Mutu a Saudiyya Yayin Aikin Hajjin 2023
A wani rahoton kuma mun samu labarin Allah ya karɓi rayuwar Alhazan Najeriya 6 rasuwa yayin aikin Hajjin bana 2023 a ƙasa mai tsarki.
Shugaban tawagar likitoci na NAHCON a hajjin 2023, Usman Galadima ne ya bayyana haka a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, yayin wani taron hukumar a garin Makkah.
Asali: Legit.ng