Gwamnati Za Ta Ruguza Gine-Gine, Ta Tsallake Wuraren da Kwankwaso Ya Saida a Kano

Gwamnati Za Ta Ruguza Gine-Gine, Ta Tsallake Wuraren da Kwankwaso Ya Saida a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano Kano ta yi haramar ruguza wasu gine-gine da ta ce an yi a kewayen badala
  • Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya saida filayen da aka yi kusan duk ginin da ake neman rusawa
  • Mutane su na zargin ana nuna son kai domin da alama ba za a taba wasu wuraren dabam a badalar ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - A ranar Juma’ar nan ne gwamnatin jihar Kano ta ayyana wasu gine-gine a cikin wadanda za a ruguza saboda zargin sun tare badalar garin.

A rahoton da Premium Times ta fitar, an ji cewa ana zargin an yi wadannan gine-gine ne a filayen da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta saida.

Abin mamakin shi ne an tsallake wasu cikin shaguna da sauran ginin da aka yi a filayen da aka saida a lokacin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Aka Sanya Cikin Wadanda Za a Rusa, Rimingado Ya Magantu

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: @EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Jama’a sun nuna mamakinsu a kan yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kyale wasu wuraren da tsohuwar gwamnatinsu ta saida a 2011-2015.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce an yi haka tun a gwamnatin farko ta Kwankwaso, amma da Malam Ibrahim Shekarau ya zama a 2003, bai rusa gine-ginen mutane ba.

Masu zargin gwamnati da son kai sun ce a lokacin Abba Yusuf ya na Kwamishina, an yanka filayen badala daga Kofar Fanfo har zuwaKofar Kabuga.

Da Ganduje ya samu mulki, sai ya saida fuloti daga Kofar Fanfo zuwa Kofar Nasarawa. A halin yanzu wadannan gine-gine ne gwamnati za ta rusa.

Akwai son kai a lamarin?

Mukhtar Mudi Sipikin ya zanta da Legit.ng Hausa a kan wannan batu, ya ce gwamnatin Kwankwaso ta yanka filaye, amma ba a tanka su ba.

‘Dan siyasar ya ce a Kantin Kwari, an yi irin haka daga Kofar Mata zuwa Hauren Balagu, haka zalika an saida shaguna a filin wasa da ke Kofar mata.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Abba Gida Ya Yi Makin Shaguna Da Gidajen Mai Na Miliyoyin Naira Cikin Wadanda Za a Rushe

Maganar da ake yi, hukumar KNUPDA ba ta da niyyar rushe wadannan gine-gine da shagu da aka yi kafin Abdullahi Ganduje ya zama Gwamna a 2015.

Idan za ayi afuwa, Sipikin ya na ganin ya kamata gwamnati ta yafewa kowa, muddin ba haka aka yi ba, ya ce za ayi zargin akwai rashin adalci a lamarin.

Gwamnati ta na da ikon yin bincike domin hukunta masu laifi a gwamnatin Ganduje, ya kara da cewa bai kamata aika-aikarsu ta shafi mutanen gari ba.

Da yake magana a Facebook, ya ce:

“Da wata hujja za ka gamsar da ni cewa, gine-ginen da akai daga Na'isa zuwa ƙofar Famfo ba dai-dai ba ne, kuma gine-ginen da suka faro daga ƙofar Famfo zuwa Kabuga dai-dai ne?”

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng