Gwamna Alia: Dole Mu Kwato Dukiyar Gwamnati da Tsohon Gwamna da Hadimansa Suka Wawure

Gwamna Alia: Dole Mu Kwato Dukiyar Gwamnati da Tsohon Gwamna da Hadimansa Suka Wawure

  • Gwaman jihar Benuwai ya lashi takobin dawo da duk wata kadara da yake ganin tsohuwar gwamnati ta yi sama da faɗi da ita
  • Ya kaddamar da kwamitin dawo da dukiyar gwamnati a matakin jiha da kananan hukumomi a Makurdi
  • Ya ce abinda suka shirya yi ba bita da kulli bane ko zaluntar wani, zasu yi ne don gyara barnar da aka tafka a baya

Benue - Gwamnan Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya buƙaci kwamitin da ya kafa ya tabbata ya kwato duk wata kadara da ake zargin tsohuwar gwamnatin Samuel Ortom ta sace ba bisa ka'ida ba.

Gwamnan ya faɗi haka ne a gidan gwamnatinsa da ke Makurɗi yayin kaddamar da shugaba da mambobin kwanitin kwato kadarorin gwamnati na jiha da kananan hukumomi.

Gwamnan jihar Benuwai a wurin kaddamar da kwamitin.
Gwamna Alia: Dole Mu Kwato Dukiyar Gwamnati da Tsohon Gwamna da Hadimansa Suka Wawure Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamna Alia na cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Haramta Ayyukan 'Yan Acaba a Babban Birnin Jiha, Ya Faɗi Dalilai

"Ba bita da kulli ko zaluntar wani zamu yi ba, sai dai mu ce zamu gyara kuskuren da aka tafka domin tattara duk wasu kadarorin gwamnati."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa gwamna Alia ya kafa kwamitin?

Alia ya ƙara da cewa ya zama wajibi ya kafa wannan kwamitin bisa la'akari da manyan motoci na alfarma da aka ga muƙarraban tsohuwar gwamnati na wataya wa da su.

A cewarsa, abin mamakin bayan ya karɓi mulki babu ko ɗaya daga cikin waɗan nan motoci duk da kowa ya san da kuɗin baitulmali aka cefano su.

Bugu da ƙari, ya ce ya sami cikakkun bayanan yadda aka yi sama da faɗi, cin mutunci da kuma wawure dukiyar gwamnatin jihar Benuwai ba kunya bare tsoron Allah.

Sakamakon haka yake ganin ya dace ya ɗauki wani mataki na dawo da dukkan waɗan nan kadarori mallakin jihar Benuwai amma wasu suka halasta wa kansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35 da Wasu Hadimai da Ya Naɗa

Shugaban kwamitin ya ɗauki alƙawari

Da yake jawabi a madadin mambobi baki ɗaya, shugaban kwamitin, Hinga Biem, ya yi wa gwamna Alia alƙawarin zasu ba shi goyon baya 100 bisa 100 domin yi wa jiha aiki.

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi a Benue

A wani rahoton mun kawo muku cewa Jam'iyyar PDP ta caccaki gwamna Alia da APC mai mulki kan matakin dakatar da ciyamomin kananan hukumomi 23.

PDP ta ce gwamna da majalisar dokokin Benuwai sun shiga ruɗani domin tuni Kotu ta hana dakatar da ciyamomin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel