Sabon ‘Dan Majalisa Ya Fara Yi wa Mutanen Mazabarsa Alheri Daga Rantsar da Shi

Sabon ‘Dan Majalisa Ya Fara Yi wa Mutanen Mazabarsa Alheri Daga Rantsar da Shi

  • Mutanen mazabar Chikun/Kajuru sun fara murna da wakilcin Ekene Abubakar Adams a Majalisa
  • Kafin ya gyara zama a Majalisar wakilan tarayya, ‘dan siyasar ya soma cika alkawuran kamfen
  • Hon. Ekene Abubakar Adams ya gaje kujerar Umar Yakubu Barde bayan nasararsa a LP a 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - ‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru a majalisar wakilan tarayya, Ekene Abubakar Adams, ya rabawa mutanensa kaya iri-iri.

Leadership ta ce Hon. Ekene Abubakar Adams ya yi rabon turansfomomi 10 masu karfin 500KVA, motoci, da babura ga wadanda ke karkashin mazabarsa.

Daga cikin wadanda su ka ci moriyar alherin ‘dan siyasar har da matan shugabannin mazabun Chikun da na Kajuru, kowace ta samu kyautar N150, 000.

'Dan Majalisa
Wasu 'Yan Majalisa a bakin aiki Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

'Yan APC da PDP sun amfana

‘Yan jam’iyyun APC da kuma PDP su ci moriyar Hon. Ekene Adams na jam’iyyar adawa ta LP. Hakan ya nuna ba zai nuna wani bambancin siyasa ba.

Kara karanta wannan

Lauyoyin PDP Sun Tanadi Jami'an INEC da Shaidu 30 Domin Tsige Sabon Gwamna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ekene Adams ya yi rabon kudi ga shugabannin mazabu 66 da ke yankin na sa a Kaduna.

Da yake zanta da manema labarai a wajen rabon kayan, ‘dan majalisar ya shaida cewa ya yi wa al’ummarsa wannan ne da dukiyarsa ba na majalisa ba.

A cewar Hon. Ekene, mutane da-dama sun kawo masa kukan halin da ake ciki a mazabarsa a lokacin yana kamfe, don haka ya ga dacewar cika alkawari.

Kyawun alkawari cikawa

Jaridar ta ce Ekene ya bayyana cewa a matsayinsa na mutum mai kyauta kafin ya shiga siyasa, ya ji dadin sauke wannan nauyin da yake kan shi na alkawari.

A game da dalilinsa na taimakawa ‘yan sauran jam’iyyu, ‘dan majalisan tarayyan ya ce a matsayin shugaba, dole a tafi da kowa muddin an gama yakin zabe.

Idan har ya na kan kujerarsa, ‘dan majalisar ya ce zai cigaba da koyi da abubuwan kwarai da wanda ya gada watau Hon. Umar Yakubu Barde ya kawo.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Sanata AbdulAziz Yari Ya Yi Wa Wasu Zamfarawa Tagomashin Alkhairi

Sarkin Kufana Kajuru, Mai martaba Titus Dauda ya yi jawabi wajen taron a madadin Sarakuna, ya na mai godewa sabon ‘dan majalisar na Chikun da Kajuru.

Dauda ya ce ba su taba ganin romon damukaradiyya irin wannan a tsawon tarihin siyasarsu ba.

Hare-haren sallar idi

An ji labari DSS ta na kira ga jama’a su kara sa ido, su kai karar duk wani motsi ko mutanen da ake zargi su na neman kai hari yayin da ake shirye-shiryen idi.

Dole ayi hattara a wuraren taron jama’a kamar kasuwanni, shaguna da sauransu a lokacin sallar bana domin jami’an tsaro sun tsinci bama-bamai kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng