Lauyoyin PDP Sun Tanadi Jami'an INEC da Shaidu 30 Domin Tsige Sabon Gwamna

Lauyoyin PDP Sun Tanadi Jami'an INEC da Shaidu 30 Domin Tsige Sabon Gwamna

  • Sa’idu Umar ya na shari’ar da Ahmad Aliyu, APC da Hukumar INEC a kan zaben Jihar Sokoto
  • Lauyoyin ‘dan takaran na PDP za su kira mutum 31 su bada shaida a shari’ar karar zaben Gwamna
  • Bayan an soma sauraron shaidun jam’iyyar PDP, kotun korafin ta dakatar da zama zuwa watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sokoto - ‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan jihar Sokoto a 2023, Sa’idu Umar, ya tanadi shaidu da za su bada shari’a a kotun karar zabe.

A rahoton PM News aka ji cewa Sa’idu Umar zai gabatar da shaidu 31 wanda za su bada shaida da nufin kotu ta ruguza nasarar da jam’iyyar APC ta samu.

Ubandoma ya na kalubalantar Mai girma Gwamna Ahmad Aliyu, Mataimakinsa, Idris Gobir da jam’iyyarsu ta APC mai mulki da kuma Hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

Zaben Gwamnan Sokoto
Yakin zaben PDP a Sokoto a 2023 Hoto: Abubakar Umar Mazara Tambuwal
Asali: Facebook

‘Dan takaran jam’iyyar adawar ya shaida haka da yake bayani a kotu ranar Alhamis a Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shaidun Jam'iyyar PDP

Daga cikin shaidun da za a kira su bada hukunci a kotun har da Ibrahim Abdulahi wanda shugaban wata makarantar firamare ne da ke garin Sabon Birni.

Shugaban rikon kwarya na sashen fasahar zamani na INEC ta reshen Sokoto, Abubakar Usman da wasu wakilan PDP a zaben su na cikin shaidun.

Rahoton ya ce Shugaban kotun sauraron korafin zaben Gwamnan, Haruna Mshelia, ya yi kira ga jama’a su yi wa dokar kasa biyayya a shari’ar da ake yi.

"Ana yi mana barazana"

Mai shari’a Haruna Mshelia ya yi wannan magana ne da yake tanka kukan da shugaban lauyoyin jam’iyyar PDP, Sunday Ameh SAN ya kawo masa.

Ameh SAN ya nuna cewa su da wasu shaidun su na fuskantar barazana a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Jam’iyya Ta Fara Shirin Gyara, Wike Sun Cigaba da Bada Matsala Wajen Sulhu a PDP

A matsayinsa na shugaban Alkalan kotun zaben, Haruna Mshelia yake cewa Sokoto gari ne na mutane masu daraja, bai kamata a rika yin abin da bai dace ba.

A zaman da aka yi, Lauyan PDP ya gabatar da Abdulmumini Usman wanda shi ne babban jami’in gudanarwa na hukumar INEC ta Sokoto a matsayin shaida.

Jecob Ochidi SAN da Hassan Liman SAN su ne Lauyoyin wadanda ake tuhuma a kotun korafin. Sai 11 ga watan Yuli za a cigaba da sauraron shari’ar nan.

Siyasar APC da Tinubu

Jigo a tafiyar Bola Tinubu yana so jagoran G5, Nyesom Wike ya sauya-sheka zuwa APC, an ji labari Tony Okocha ya na zawarcin tsohon Gwamnan Ribas.

Shugaban kungiyar BAT-Vanguard a Kudu maso kudu ya ce Wike ya cancanci Bola Tinubu ya ba shi mukami saboda irin gudumuwarsa a a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng