Kano: Abba Gida Gida Ya Bada Umurnin A Bincike Kudaden Da Ake Cire Wa Daga Albashin Ma'aikata
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin dakatar da cire kudaden ma'aikata a jihar ba bisa ka'ida ba
- Gwamnan ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Bichi ya sanya wa hannu
- Gwamnan ya kuma umarci dakatar da cire kudaden shiga har kashi 16.25 na asibitocin gwamnati na birnin Kano
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci a yi binciken gaggawa kan zaftarewa ma'aikata albashinsu a jihar.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Bichi ya sanya wa hannu.
Daya daga cikin sanarwar ta umarci dakatar da cire kudaden ba bisa ka'ida ba har N370 akan kowa ne ma'aikaci da kuma 'yan fansho a jihar, TheCable ta tattaro.
Sanarwar ta kara da cewa kudaden da ake cirewa ana tura su ne zuwa wani kamfani mai sune Share Benefit Investment Limited.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Kabir ya ba da umarnin dakatar da cire kudaden ma'aikata
A cewar sanarwar:
"Gwamnati ta gano yadda ake cirewa ma'aika kudade na N370 a albashi da kuma fansho na ma'aikata.
"Wannan kudade da ake cirewa ba bisa ka'ida ba ana tura su ne zuwa wani kamfani Share Benefit Investment Limited.
"Dalilin haka, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin dakatar da cire wadannan kudade ba bisa ka'ida ba.
"Hai ila yau, ya ba da umarnin dawo da kudaden da kamfanin ya karba har zuwa lokacin da za a kammala binciken dalilin cire kudaden.
Gwamnan ya kuma ba da wata umarni na daban kan asibitocin Kano
A wata sanarwar ta daban, gwamnan ya kuma umarci dakatar da cire kashi 16.25 daga kudaden shiga na asibitocin gwamnati da ke birnin Kano.
Sanarwar ta kara da cewa kudaden da ake cirewan ana tura su ne zuwa wani kamfani na ICT Global System da bankin Polaris, cewar Daily Trust.
Tun bayan hawan Abba Kabir Yusuf karagar mulki ya ke ta binciken tsare-tsaren da tsohon gwamna Ganduje ya dabbaka don tabbatar da ingancinsu.
Gwamnan Kano Ya Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO Don Inganta Ilimi
A wani labarin, gwamnatin jihar Kano ta biyawa dalibai 55,000 kudaden jarrabawar NECO.
Gwamnan jihar, Abbab kabir Yusuf shi ya bayyana haka a wata sanarwa da sakataren yada labarai a jihar, Sanusi Bature ya fitar.
Ya ce biyan kudaden ga dalibai an yi shi ne don inganta harkar ilimi a jihar da take neman rugujewa.
Asali: Legit.ng