Tsohon Minista Ya Yabi Tinubu a Kan Irin Nade-Naden Mukaman da Yake Yi a Mulki

Tsohon Minista Ya Yabi Tinubu a Kan Irin Nade-Naden Mukaman da Yake Yi a Mulki

Festus Keyamo ya yabi Bola Ahmed Tinubu bayanin ganin irin mutanen da yake nadawa a gwamnati

Tsohon Ministan ya ce ayyukan da sabon Shugaban kasan ya fara ya jawo masa kaunar makiyansa

Keyamo, SAN ya tabo maganar wata shari’a da ya yi da Shugaban kasa Goodluck Jonathan a kotu

Abuja - Tun kafin a je ko ina, tsohon Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya, Festus Keyamo ya yabi kamun ludayin Bola Ahmed Tinubu.

Da yake magana a shafinsa na Twitter a makon nan, Festus Keyamo SAN ya ce har ‘yan adawa sun fara yabon salon shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

Keyamo wanda shi ne Kakakin yakin neman zaben Bola Tinubu a APC, ya ce tun farko sun hango za a zo rana irin ta yau, da ake yabon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Mataimakin Buhari, Farfesa Osinbajo Ya Samu Aikin Farko Bayan Barin Aso Rock

Shugaban kasa
Shugaban kasar Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwararren Lauyan ya tofa albarkacin bakinsa ne da ya saurari bidiyon wata masoyiyar LP, Chioma Olowo ya na ba Peter Obi shawarar ya bi bayan Tinubu.

Legit.ng Hausa ta fahimci Chioma Olowo ta yi kira ga Obi ya janye karar da yake yi a kan zaben 2023, a cewarta Tinubu ya na kokari a kan karagar mulki.

Keyamo ya ce sun san za a rina

"Yadda Bola Ahmed Tinubu ya fara mulki da kyau ya na cigaba da burge mutane da-dama, har manyan ‘yan adawarsa, sun fara kaunarsa.
Wasunmu sun hango cewa za a zo nan."

-Festus Keyamo

Daga baya ‘dan siyasar ya yi dogon rubutu a dandalin sada zumuntan, ya na cewa duka wadanda su ka samu mukami a gwamnatin Tinubu, sun cancanta.

Shari'ar Keyamo v Gwamnati

Baya ga haka kuma Keyamo ya bugi-kirji ya na cewa ya ji dadin ganin yadda ake yi wa dokar kasa biyayya tun bayan wata shari’arsa da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

A cewar Lauyan, shi ya kalubalanci Goodluck Jonathan cewa dole sai majalisa ta tantance hafsun sojoji kafin su iya fara aiki, kuma ya yi nasara a gaban kotu.

Duk wani mutum da Bola Tinubu ya ba mukami, ya cancanta da kujerarsa. Ina kuma farin ciki da gwamnatin tarayya ta ke cigaba da bin hukuncin kotu.
A shari’ar Keyamo da Shugaban kasar tarayyar Najeriya, na kalubalanci ikon shugaban kasa wajen nada hafsun sojoji ba da izinin ‘yan majalisar tarayya ba.

-Festus Keyamo

Karin albashi a Najeriya

A rahoton nan, an ji yadda Gwamnatin Bola Tinubu ta nuna niyyarta na duba bukatun da Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC su ka gabatar mata.

‘Yan kwadago su na so a tanadi motocin haya masu aiki da gas kuma ayi wa ma’aikata karin albashi a sakamakon janye tallafin man fetur da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng