Kwana Nawa Tinubu Zai Dauka? Kwanakin Da Obasanjo, Jonathan Da Buhari Suka Yi Kafin Nada Ministoci

Kwana Nawa Tinubu Zai Dauka? Kwanakin Da Obasanjo, Jonathan Da Buhari Suka Yi Kafin Nada Ministoci

  • Bayanai sun bayyana kan adadin kwanakin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya ɗauka kafin ya aika da sunayen ministocinsa ga Majalisar Dattawa
  • Rahoto ya nuna cewa, Buhari ne ya fi ɗaukar mafi yawan kwanaki kafin aikawa da sunayen ministocinsa zuwa majalisa
  • Obasanjo a wa'adinsa na farko, ya kafa tarihin aikawa da sunayen ministocin nasa zuwa majalisa a cikin mako guda da rantsar da shi

Bayanai sun fito kan tsawon lokacin da tsaffin shugabannin ƙasa, Obasanjo, Umaru Yar’adua, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari suka ɗauka kafin su aika da sunayen ministocinsu ga Majalisar Dattawa bayan hawansu karagar mulki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke dakon ministocin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai naɗa.

Kwanakin da tsoffin shugabanni suka dauka wajen nada ministoci
Kwanakin da Obasanjo, Jonathan da Buhari suka dauka kafin nada ministoci. Hoto: Goodluck Jonathan, Asiwaju Bola ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kwanakin da Obasanjo da Umar Yar'adua suka ɗauka kafin naɗa ministocinsu

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Hakeem Odumosu A Matsayin Shugaban Hukumar EFCC? Gaskiya Ta Bayyana

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, Obasanjo ya kwashe kwanaki shida ne kacal kafin ya aika da sunayen ministocinsa ga Majalisar Dattawa a ranar 4 ga watan Yuni, 1999.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma a wa’adinsa na biyu, Obasanjo ya shafe kwanaki 25 kafin ya aika da sunayen ministocinsa ga Majalisar Dattawa, wanda ya yi a ranar 23 ga Yuni, 2003.

Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua, wanda ya karɓi mulki daga hannun Obasanjo, ya jira har zuwa ranar 27 ga Yuli, 2007, wato kwanaki 59 kenan da hawansa mulki.

Kwanakin da Goodluck Jonathan da Buhari suka ɗauka kafin naɗa ministocinsu

Goodluck Jonathan ya kwashe kwanaki 30 kafin ya aika da sunayen ministocin nasa zuwa Majalisar Dattawa a ranar 28 ga watan Yuni, 2011 bayan rantsar da shi da aka yi a ranar 29 ga watan Mayun, 2011.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode

Shugaban ƙasar da ya fi daɗewa wajen aikawa da sunayen ministocinsa zuwa Majalisar Dattawa tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999 Shi ne Muhammadu Buhari.

Bayan rantsuwa a 29 ga watan Mayun 2015, Buhari ya jira har zuwa ranar 30 ga watan Satumba, kwanaki 124 bayan hawansa mulki, kafin aikawa da sunayen ministocin.

An samu ci gaba a wa’adinsa na biyu, inda ya aika da sunayen ministocin ga Majalisar Dattawa cikin kwanaki 54, a ranar 22 ga Yuli, 2019.

Abin tambaya a yanzu shi ne, yaushe ne shugaba Bola Tinubu zai sanar da ministocinsa. Ku tuna cewa Majalisar Dokokin ƙasa ta zartar da wani kudirin doka na cewa dole ne a naɗa ministoci cikin kwanaki 60 na farko da shugaban ƙasa ya hau karagar mulki.

Rikicin cikin gida na neman ɓarkewa a APC game da naɗin ministoci

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto kan cewa, rikicin cikin gida na neman ɓarkewa a cikin jam'iyyar APC mai mulki kan muƙaman ministocin da ake jira Shugaba Tinubu ya bayar.

Kara karanta wannan

Sabon Rahoto Ya Bayyana Matsayin Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Ba Kwankwaso A Majalisar Ministocinsa

Rahotanni daga jihohi na nuni da cewa, tsofaffin gwamnoni da shuwagabannin jam'iyyu na hanƙoron ganin cewa sun shiga cikin ministocin na Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng