Jam’iyya Ta Fara Shirin Gyara, Wike Sun Cigaba da Bada Matsala Wajen Sulhu a PDP

Jam’iyya Ta Fara Shirin Gyara, Wike Sun Cigaba da Bada Matsala Wajen Sulhu a PDP

  • Shugabannin majalisar NWC sun cigaba da zama da jagororin jam’iyyar PDP baya zaben 2023
  • Hikimar zaben ita ce shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye jam’iyya, a samu hadin-kan kowa
  • Shugaban PDP yake cewa da farko an yi niyyar zaman ne da wadanda aka kafa jam’iyya da su

Abuja - A yunkurin canza yadda abubuwa su ke tafiya a PDP, shugabannin majalisar gudanarwa na NWC sun yi zama na musamman a garin Abuja.

Premium Times ta rahoto cewa dalilin zaman shi ne a sasanta sabanin da ke tsakanin jagororin jam’iyya ganin abubuwan da su ka faru a zabe.

Ambasada Umar Damagum ya jagoranci zaman a matsayinsa na shugaban rikon kwarya na PDP.

Jam’iyyar PDP
Titi, Atiku, Secondus, Okowa a taron Jam’iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Umar Damagum yake cewa taron zai bada dama a duba yadda abubuwa su ka faru a zaben da ya gabata sai kuma a duba hanyoyin da za a bi wajen gyara.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban jam’iyyar na kasa yaa kara da cewa kafin yanzu sun yi zama da wasu shhugabanni na kasa, shugabannin jihohi, BOT da kuma ‘yan majalisa.

Jawabin Umar Damagum

"Wannan ya na cikin taron da ake yi domin shirye-shiryen gobe. Da farko an yi niyyar yin zaman ne da wadanda aka kafa jam’iyya da su kurum.
Daga baya sai mu ka fahimci bayan tsawon shekaru 20 da kafuwa, wasu mutane da-dama sun girma, an yaye su, sun zama iyayen jam’iyyar PDP."

- Umar Damagum

Manya Jam'iyya sun hallara

Rahoton ya ce PDP ta tuna da tsofaffin Gwamnonin jihohi wadanda su ka taka rawar gani. A mako mai zuwa ne za a fara zama da mata da matasan PDP.

Wadanda su ka yi jawabi a wajen taron sun hada da Sakataren gudanarwa na kasa, Umar Bature da kuma shugaban majalisar amintattu, Adolphus Wabara.

Kara karanta wannan

Yadda Na Samu Kudi, Na ba Wike Gudumuwar Takarar N200m – Shugaban Majalisa

Ina 'Yan G5 da Tambuwal?

Punch ta ce Nyesom Wike, Ifeanyi Ugwuannyi da Aminu Tambuwal ba su zo ba, amma Uche Secondus wanda bai samu halarta ba, ya aiko uzurinsa.

Udom Emmanuel, Bukola Saraki, Gwamna Godwin Obaseki, Bode George da Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da-dama sun halarci wannan taro da aka yi.

Haka zalika an ga tsohon shugaban PDP, Ahmed Makarfi da tsohon Minista, Maina Waziri.

Gudumuwar Godswill Akpabio

A baya an ji labari Nyesom Wike ya jefa shugaban majalisar dattawa a matsala da ya fallasa kyautar kudin Godswill Akpabio ya ba shi a lokacin takararsa.

Daga baya Sanata Akpabio ya fadi silar Naira Miliyan 200 da ya bada a matsayin gudumuwar kamfe, ya ce ba dukiyar al’ummar Akwa Ibom ya sata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng