Watakila Bola Tinubu Ya Jefar da Tsofaffin Gwamnoni Wajen Nada Sababbin Ministoci

Watakila Bola Tinubu Ya Jefar da Tsofaffin Gwamnoni Wajen Nada Sababbin Ministoci

  • Babu tabbacin tsofaffin Gwamnonin jihohi za su samu shiga cikin jerin sababbin Ministocin tarayya
  • Wajen zaben Ministoci, da alama zuciyar Bola Tinubu ta fi karkata ga kwararru kan zallar ‘yan siyasa
  • Wadannan ‘yan siyasa su na ganin sun bada gudumuwa a jam’iyyar APC har Tinubu ya hau mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A lokacin da ‘yan siyasa su ke kara huro wuta domin samun kujerar Minista, ana tunanin Bola Ahmed Tinubu ya na da ra’ayi na dabam.

Rahoton da aka samu daga Vanguard ya shaida cewa Bola Ahmed Tinubu bai so ya cika kujerun Ministoci da tulin tsofaffin gwamnoni ‘yan siyasa.

Wata majiya ta ce shugaban kasar ya fi sha’awar ya yi aiki da kwararru a ma’aikatun tarayya. A Kudu kuma ya samu sabani da wasu gwamnoni.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

Bola Tinubu
Shugaban kasa a wajen taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan ya jawo ake tunani Bola Tinubu ba zai ba wasu daga cikin Gwamnonin da su ka sauka daga mulki a Mayu mukami a majalisar zartarwa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mecece mafitar tsofaffin Gwamnoni?

A halin yanzu akwai tsofaffin Gwamnoni daga jam’iyyun APC mai mulki da PDP mai adawa da su ke kamun kafar samun Minista ko wata kujerar.

Baya ga Ministoci akalla 36 da za a nada, akwai mukamai a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya bayan an ruguza majalisunsu.

Jaridar ta ce akwai tsofaffin Gwamnoni musamman daga jihohin Arewacin Najeriya da ke harin mukamai, amma shugaban kasar yana ta guje masu.

Wani na kusa da fadar shugaban kasa ya nuna cewa ‘yan siyasan su na so su kawo wadanda za a ba mukamai, sannan su tsira da matsayin Ministoci.

An ci moriyar ganga?

Halin da ake ciki a jam’iyyar APC shi ne wasu da suka yi mulki a jihohin Arewa sun zama karfen kafa ga Bola Tinubu ganin tasirinsu ya ragu a siyasa.

Kara karanta wannan

Jirgin Bola Tinubu Ya Sauka a Faransa, An Ji Ranar da Shugaban Kasa Zai Dawo Najeriya

Duk da sun gagara taimakawa APC mai-ci wajen samun nasara a jihohinsu da su ke kan mulki, tsofaffin Gwamnonin su na ganin sun taimaki Tinubu.

Akwai wadanda sun karbi kudin kamfe wajen Shugaba Tinubu a lokacin zabe, sannan majiyar ta ce yanzu su na neman kwangiloli a Aso Rock.

"Omo Agege ya ci amana"

Wasu jagororin jam’iyyar APC a Delta sun rubutawa Bola Tinubu wasika a kan Ovie Omo Agege, an ji labari su na zarginsa da lafin yakar Shugaban kasar.

‘Yan siyasar sun fallasa yadda tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kawo Godwin Emefiele domin hana Bola Tinubu nasara a zaben gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng