Wike Ya Bayyana Yadda Aka Zuba Masa Guba A Sakatariyar PDP A Abuja

Wike Ya Bayyana Yadda Aka Zuba Masa Guba A Sakatariyar PDP A Abuja

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nwesom Wike ya bayyana irin kalubalen da rinka gamuwa da su a siyasa wadanda bai taba fadawa kowa ba
  • Wike ya bayyana haka ne yayin bikin godiya na musamman da aka shirya dominsa bayan kammala gwamnatinsa tare da mika mulki lafiya
  • Tsohon gwamnan ya bayyana yadda aka zuba masa guba da ya kusa kawo karshen rayuwarsa a watan Disamba na shekarar 2018

Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana yadda aka saka masa guba a sakatariyar jam'iyyar PDP a watan Disamba na shekarar 2018.

Wike ya bayyana haka ne yayin bikin godiya na musamman da aka shirya masa a St. Deanery a karamar hukumar Obio-Akpor da ke jihar.

Wike ya ce an zuba masa guba a sakatariyar PDP a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom. Hoto:Daily Trust.
Asali: Twitter

Ya ce gubar ta ratsa dukkan sassan jikinsa tare da kawo matsala a hanta da kuma kodarsa inda ya ce idan ba ikon Allah ba da ya mutu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Wike ya ce a dalilin gubar har kodarsa da hantarsa sun samu matsala

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A shekarar 2018, rana ta karshe a matsayina na shugaban ma'aikata, yayin bikin godiya, tun daga rana Lahadi a wancan lokacin ban fito daga dakina ba.
"Wadanda suka halarci wannan bikin sun sani ban yi bayani ba, na zauna ne kawai na fadawa mataimakin gwamna ya yi bayani a madadi na, na dauka daga ranar shikenan."

Wike ya ce an dauke shi zuwa asibiti a Lebanon yayin da likitoci suka yi gwaje-gwaje suka tabbatar cewa hantarsa da koda duk sun bar aiki.

Ya bayyana cewa a lokacin zargin kowa yake yi inda ya yanke shawarar ba zai sake zuwa wani taro ba musamman a lokutan yakin neman zabensa, Daily Post ta tattaro.

Ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta amma bai fadawa kowa ba

Kara karanta wannan

"Maganin Kara Kuzarin Maza Ya Sha": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka a Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa, Budurwar Ta Tsere

Tsohon gwamnan har ila yau, ya bayyana wani lokaci kuma da ubangiji ya kare shi da wasu shugabanni guda uku daga hadarin jirgin sama.

Ya kara da cewa:

"Bayan mintuna 15 da fara tafiya, sai muka ji karar inji ya fashe, daya daga cikin matukan jirgin ya ce ba matsala zamu iya komawa Port Harcourt lafiya, haka muka samu muka isa cikin dar-dar, ubangiji ya taimaka, babu wanda na fadawa."

Ya ce yana boye irin wadannan munanan abubuwa da suka faru da shi don kada ya tayarwa magoya bayansa hankali don gudun yadda za su kasance.

Ba Zan Karbi Mukamin Tinubu Ba, Sai da Sharadi, Wike Ya Bayyana Matakin Gaba

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana sharuda idan Tinubu ya bashi mukami.

Wike ya ce ba zai karbi mukami ba har sai ya shawarci mai dakinsa ya ji mai zata ce game da hakan.

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Rayuwa Babu Ita Ba”: Dan Najeriya Ya Yi Wuff Da Tsohuwar Baturiya, Hotunan Su Yadu

Ya kara da cewa bayan ita, zai tuntubi 'yan uwa da abokan arziki da ya yarda da su don jin ta bakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.