Har Yanzu Peter Obi Ya Fi Tinubu, Atiku Da Saura, In Ji Obasanjo, Ya Bada Dalili
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu bai yadda cewa Bola Tinubu zai iya kawo sauyin da kasar ke bukata ba a halin da ake ciki
- Tsohon shugaban kasar, ya ce har yanzu bai ga wanda ya dace kamar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ba don gyara kasar
- Obasanjo tun a farkon lokacin fara gangamin yakin neman zabe, ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi inda ya ce ya fi dukkan sauran cancanta
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tabbatar da cewa har yanzu babu dan takarar da ya fi Peter Obi cancanta a zaben da aka gudanar.
Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a wata ganawarsa da dan jarida Chude Jideonwo, Legit.ng ta tattaro.
Duk da sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben, Obasanjo ya ce duk da haka Peter Obi yafi shi dacewa.
"Maganin Kara Kuzarin Maza Ya Sha": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka a Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa, Budurwar Ta Tsere
Obasanjo ya ce Peter Obi yafi sauran 'yan takara cancanta
Ya ce dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi shi ne dan takara mafi cancanta da dacewa a cikin sauran 'yan takarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa shi ne kadai yake da kwarewa wurin kawo sauyi a kasar musamman ayyukan yi ga matasa, cewar Tribune.
A cewarsa:
"Najeriya da na sani a wannan lokaci, babu wanda muka fi bukata kamar Peter Obi, shi ne yafi kowa."
Peter Obi na daga cikin 'yan takarar da ke kalubalantar zaben da aka gudanar
Idan ba a mantaba, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu.
Peter Obi na daya daga cikin wadanda suke kalubalantar zaben, inda suke zargin an tafka magudi da kuma kura-kurai yayin tattara sakamakon zaben.
Gaskiya Ta Bayyana Kan Batun Obasanjo Ya Yi Hayar Lauya Don Kare Peter Obi
A wani labarin, gabannin fara korafe-korafen zaben da aka gudanar ance tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya taimaki Peter Obi.
Ana zargin Obasanjo da dauko hayar wata lauya 'yar kasar Rasha don kalubalantar zaben da aka gudanar.
Amma daga bisani Obasanjo ya musanta wannan zargi ta bakin hadiminsa Kahinde Akinyemi.
Asali: Legit.ng