Abdulaziz Yari: 'Wasu Takwarorina Sun Ci Amanata Yayin Zaben Shugaban Majalisa Ta 10'

Abdulaziz Yari: 'Wasu Takwarorina Sun Ci Amanata Yayin Zaben Shugaban Majalisa Ta 10'

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa yana ji a ransa kamar an yaudaresa a zaɓen shugabannincin majalisa ta 10 da ya gabata
  • A zaɓen da aka gudanar ranar Talata da ta gabata, Sanata Godswill Akpabio ne ya yi nasarar zama shugaban Majalisar Dattawa da ƙuri’u 63, a yayin da Yari ya samu kuri’u 46
  • Yari ya yi adawa da zaɓin jam’iyyar APC, kuma ya yi iƙirarin samun goyon bayan kashi 70 cikin 100 na Sanatoci amma a ƙarshe ya sha kaye a zaɓen Shugaban Majalisar Dattawan

Abuja - Babban ɗan takaran kujerar shugabancin Majalisar Dattawa ta 10, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce yana ji kamar an yaudare shi a zaɓen shugabancin Majalisar ta 10 da ya gabata.

A yayin ƙaddamar da majalisar ta 10, sanatoci sun zaɓi sabon shugaba, inda Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban Majalisar Dattawan da ƙuri’u 63, a yayin da abokin hamayyarsa Abdulaziz Yari ya samu ƙuri’u 46.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Yaudara ta aka yi a wajen zaben
Sanata Abdulaziz Yari ya ce yaudararsa wasu sanatocin suka yi a zaɓen Majalisar Dattawa. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Yari ya sha kaye duk da iƙirarin goyon bayan kashi 70 cikin 100 na Sanatocin

Duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ya zaɓi Akpabio da Barau Jibrin a matsayin shugaban Majalisar Dattawa da mataimakinsa, Yari ya yi adawa da zaɓin, inda ya yanke shawarar fitowa a fafata da shi, kamar yadda rahoton The Punch ya bayyana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan watsi da duk wasu kiraye-kiraye na jam’iyyar, da kuma iƙirarin cewa yana da goyan bayan kashi 70 cikin 100 na sanatocin, Yari ya fafata da Akpabio, inda ya sha kaye a zaɓen shugabancin Majalisar Dattawan ta 10.

Da yake mayar da martani kan kayen da ya sha a wata ganawa da manema labarai, Yari ya ce yana jin kamar an yaudare shi game da sakamakon zaɓen, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

Sanata Yari, wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne ya ce:

"Zan iya cewa an yaudare ni saboda a lokacin da muke yin lissafin da karfe 3 na daren ranar Talata kafin zaɓen, mun yi lissafin sama da sanatoci 76 a cikin tawagarmu."
"Mun fahimci cewa za a iya samun wasu 15 daga cikin da ka iya juya mana baya, mun aminta cewa duk da hakan, muna da guda 61."
"Amma abin da muka samu akasin hakan ne, kuma ina ji cewa an yaudare ni ne a sakamakon zaɓen da na gani."

Yari ya yi alƙawarin yin aiki tare da Sanata Akpabio

Sanata Yari, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki da sabon shugaban Majalisar Dattawan, domin yi wa ‘yan Najeriya aiki da gina Majalisar Dattawan.

A kalamansa:

“Rayuwa juyi-juyi ce, kuma a matsayina na Musulmi, Allah ne ya yanke hukunci kan wanda zai zama shugaban Majalisar Dattawa ta 10, kuma ba ni da dalilin da zai hana in yarda da hukuncin da Allah ya yanke.”

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Gwamnonin APC, PDP Da Suka Halarci Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10

"Na bai wa shugaban Majalisar Dattawan tabbacin cewa za mu yi aiki tare don kare wannan babban gida da muke da."

Tinubu ya gana da Sanusi Lamido Sanusi

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, Shugaba Tinubu ya yi wata ganawa da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sunusi Lamido Sanusi, ranar Alhamis, a fadar gidan gwamnati da ke Abuja.

Ganawar dai ita ce ta farko a tsakaninsu tun bayan rantsar da sabon shugaban ƙasar da ta gudana a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng