Na Kusa Da Atiku Abubakar Ya Hango Wani Babban Kuskure Da Shugaba Tinubu Ya Yi
- Na hannun daman Atiku Abubakar ya caccaki Shugaba kan jawabin da ya yi na ranar dimokuraɗiyya a ranar 12 ga watan Yuni
- Daniel Bwala ya ce shugaban ƙasar ya yi kuskure saboda ƙin ambatar Atiku Abubakar a cikin jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya
- Kakakin yaƙin neman shugaban ƙasan na PDP ya kuma ce sunan Peter Obi yakamata ya fito a cikin jawabin na shugaba Tinubu
FCT, Abuja - Kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Daniel Bwala, ya caccaki shugaba Tinubu saboda ƙin ambatar Atiku Abubakar da Peter Obi, a cikin jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.
Bwala ya bayyyana hakan ne a yayin wata tattauna da gidan talbijin na Channels tv a shirin Politics Today ranar Laraba.
Shugaba Tinubu shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda Atiku na PDP da Peter Obi na Labour Party, suka zo na biyu da na uku. Dukkaninsu suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu.
Bwala ya ce shugaba Tinubu ya yi kuskure
"Ta yaya za ka yi maganar dimokuraɗiyya da yaƙin kafa dimokuraɗiyya a Najeriya ba tare da ka ambaci Atiku Abubakar ba?" A cewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban ƙasa bai ambaci Atiku Abubakar, wanda hakan a wajena ba hanyar kawo haɗin kai bace."
Bwala ya yi nuni da cewa ranar rana ce ta murnar rayuwa da faɗin tashin da Cif Moshood MKO Abiola ya yi.
Zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993 ɓa shugaban ƙasa dai ana hasashen MKO Abiola ne ya lashe shi. A shekarar 2018, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana ranar a matsayin ranar dimokuraɗiyya, inda ta tashi daga ranar 29 ga watan Mayu.
"Yakamata kasan cewa Atiku Abubakar ne mutumin da ya janyewa Abiola a wajen zaɓen fidda gwani, daga nan kuma aka ci gaba da faɗi tashi." A cewarsa.
"A dalilin hakan na yi tunanin zai yi wannan neman sulhun. Hatta Peter Obi yakamata ya ambace shi. Saboda Peter Obi a karon farko cikin tarihi ya jagoranci kawo sauyi wanda ba mu taɓa gani ba."
Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, tsohon Sanatan PDP ya koma yabon salon mulkin da shugaba Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa.
Ben Murray Bruce ya yaba da kamun ludayin mulkin shugaba Tinubu tun lokacin da ya ɗare kan karagar mulkin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng