Shugabancin Majalisa: Ainihin Dalilin Da Yasa Tinubu Da APC Suka Goyi Bayan Akpabio, Shettima Ya Yi Bayani

Shugabancin Majalisa: Ainihin Dalilin Da Yasa Tinubu Da APC Suka Goyi Bayan Akpabio, Shettima Ya Yi Bayani

  • Mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, Kashim Shettima ya goyi bayan zaɓaɓɓun sanatoci Godswill Akpabio da Barau Jibrin a shugabancin majalisar dattawa ta 10
  • Shettima ya bayyana goyon bayan nasa ne ranar Laraba, 24 ga watan Mayu a yayin da yake jawabi ga mambobin kungiyar 'Stability Group'
  • Kungiyar dai na fafutukar ganin Akpabio da Barau sun yi nasara a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, Kashim Shettima ya bayyana ainihin dalilin da ya sanya APC da Tinubu marawa Akpabio baya.

Ya ce shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, da jam’iyyar APC mai mulki sun marawa Sanata Godswill Akpabio baya a kan shugabancin Majalisar Dattawa ne saboda daidaita Najeriya.

Kashim Shettima ya bayyana ainihin dalilin da ya sa APC da Tinubu suka tsaida Akpabio
Kashim Shettima ya bayyana ainihin dalilin da ya sa APC da Tinubu suka tsaida Akpabio. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Obot Akpabio
Asali: Facebook

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu, yayin wata ganawa da kungiyar 'Stability Group', kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zance Ya Kare: Gwamna Wike Ya Bayyana Zabinsa a Shugabancin Majalisar Dattawa Ta 10

Domin zaman lafiya da daidaita ƙasa aka zaɓi Akpabio

Shettima, mataimakin shugaba mai jiran gado, ya ce Bola Tinubu, da shugabannin jam’iyyar APC sun goyi bayan takarar Sanata Akpabio ne domin kawo daidaito a ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar 'Stability Group' kungiya ce ta yaƙin neman zaben sanata Akpabio, wacce ta ƙunshi zababbun sanatoci da dama.

Kashim Shettima ya bayyana zaɓin Akpabio a matakin mutum na uku mafi girma a Najeriya, a matsayin mafi kyawun hukunci da shugabannin jam’iyyar APC da Tinubu suka yanke, kamar yadda jaridar Vanguard ta yi rahoto.

A kalaman na Shettima:

“Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakin shugaban kasa duka Musulmi ne.”
“Yana dakyau domin samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasar nan, a bayar da matsayi na gaba ga Kiristoci, akasin haka kuma, zai tabbatarwa da mutane ajandar Musuluntarwa da ake zargin gwamnatin APC da ita.”

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Batun takarar Sanata Akpabio

Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki dai sune suka amince da tsayar da Akpabio takarar shugabancin majalisar dattawa ta ƙasa ta 10.

A farkon watan Mayu ɗin nan ne dai kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na ƙasa (NWC), ya amince da wannan tsari a yayin wani taro na musamman da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.

Sai dai wannan mataki da jam'iyyar ta ɗauka ya fuskanci ƙalubale, saboda hukuncin bai yi wa wasu masu neman takarar daɗi ba.

Wike ya goyi bayan Akpabio

Shi ma a nasa ɓangaren, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar jam'iyyar APC a shugabancin majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da zaɓaɓɓun sanatoci ƙarƙashin ƙungiyar 'Stability Group' suka kai masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel