“Orji Kalu, Izunaso Na Duba Yiwuwar Janyewa Daga Tseren Shugaban Majalisar Dattawa” - Majiya

“Orji Kalu, Izunaso Na Duba Yiwuwar Janyewa Daga Tseren Shugaban Majalisar Dattawa” - Majiya

  • Babban mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Kalu da Osita Izunaso na duba yiwuwar janyewa daga tseren shugaban majalisar dattawa
  • A cewar wata majiya mai tushe Kalu, Izunaso sun yanke shawarar janyewa daga tseren bayan tattaunawar da aka yi da su ana gab da zaben
  • Sai dai a yanzu ana ganin AbdulAziz Yari zai rage shi kadai cikin masu fafatawa a tseren

Yan awanni kafin rantsar da majalisar tarayya ta 10, Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia da Osita Izunaso, tsohon sakataren jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa suna duba yiwuwar janyewa daga tseren takarar shugabancin majalisar dattawa.

Kalu, Izunaso, da Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara sun dage cewa sai su yi takarar kuejrar shugaban majalisar dattawa duk da matsayin jam'iyyarsu.

Jiga-jigan APC
“Orji Kalu, Izunaso Na Duba Yiwuwar Janyewa Daga Tseren Shugaban Majalisar Dattawa” - Majiya Hoto: Tinubu Shettima Ambassadors - TSA Anambra State Chapter
Asali: Facebook

Orji Kalu, Izunaso suna duba yiwuwar janyewa daga takarar shugaban majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Babban Gwamnan PDP Ya Yi Hasashen Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

APC ta tsayar da Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar dattawa sannan ta zabi Jibrin Barau, sanata mai wakiltan Kano ta arewa a matsayin mataimakinsa amma jiga-jigan uku suka dage sai sun yi takara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai a wata tattaunawar karshe da aka yi da su, Kalu da Izunaso suna duba yiwuwar janyewa daga tseren bayan taron shugabannin kudu maso gabas, jaridar The Cable ta rahoto.

Zababbun sanatoci daga sauran yankunan kasar ma sun halarci taron gaggawan.

Majiyoyi sun yi karin haske

Wata majiya mai tushe wacce ke sane da abubuwan da ke faruwa ta bayyana cewa Yari na iya kasancewa shi kadai a yanzu saboda yunkurin jiga-jigan siyasar biyu na hadewa da jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

"Gaba daya zababbun sanatocin kudu maso gabas 15 sun yarda za su marawa Godswill Akpabio baya. Sun yi wata ganawa da shi inda suka yi alkawarin mara masa baya," inji majiyar.
"Haka kuma wasu zababbun sanatocin arewa musamman na APC wadanda suka ki marawa takarar Akpabio baya sun dawo hanya. Sani Musa na Neja wanda ke hararar kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa ya janyewa Barau. A yanzu Yari shi kadai ne."

Abdul Ningi, tsohon jigon majalisar dattawa, ya bayyana a makon jiya cewa Yari na da zababbun sanatoci fiye da 60 da ke goyon bayan kudirinsa.

Shugaban majalisar dattawa: Gwamnoni na tare da zabin shugaba Tinubu, Seyi Makinde

A gefe guda, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa shi da yan uwansa gwamnoni suna tare da dan takarar da shugaban kasa Bola Tinubu ke so ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba.

A ranar Talata, 13 ga watan Yuni ne za a rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 kuma a nan ne za a zabi wadanda za su jagoranci harkokin shugabanci a majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel