“Wase Nake Goyon Baya A Zuciyata, Amma Abass Na Zaba A Zahiri”, Bidiyon Dan Majalisa Mai Baki 2 Ya Bayyana
- An gudanar da zaɓen majalisar wakilai ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, inda mambobi daga jam'iyyu daban-daban suka kaɗa kuri'unsu
- Ɗan majalisa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour, honarabul Victor Afam Ogene, ya miƙe tsaye, inda ya bayyana ainihin wanda zai zaɓa a shugabancin majalisar
- A lokacin ne ya bayyana cewa ya zaɓi Tajudeen Abass, sai dai ya fayyacewa jama'a cewa, zuciyarsa na tare da Idris Wase
FCT, Abuja - Honarabul Victor Afam Ogene na jam’iyyar Labour Party ya ja hankulan jama'a zuwa garesa a wajen ƙaddamar da majalisar wakilai ta 10 da aka yi a harabar majalisar dokoki da ke Abuja.
A yayin da ake kaɗa kuri'ar zaɓen kujerar kakakin majalisar tsakanin Hon Abass Tajudeen da Hon Idris Wase, an tambayi ɗan majalisar na Labour kan ko wa zai zaɓa?
Wa Afam Ogene ya zaɓa a matsayin kakakin majalisa?
A yayin da yake bayyana wanda yake so ya zama kakakin majalisar ta 10, ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazaɓar Ogbaru ta jihar Anambra, ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duk da zuciyata tana tare da Idris Wase, kuri'ata ta tafi wurin Tajudeen Abbas ne"
Maganar da mamban ya yi ta sa an kece da dariya a zauren majalisar ta wakilai.
A zaɓen 2023 da ya gabata, Ogene ya doke ɗan majalisar wakilai mai ci a mazabar honarabul Chukwuma Onyema na jam’iyyar PDP, wanda ya kasance ya yi wa majalisar zuwa uku.
Ogene a ƙarƙashin jam’iyyar Labour ya samu ƙuri’u 10,851 daga cikin ƙuri’un da aka kaɗa, a yayin da ɗan takarar jam’iyyar PDP, honarabul Chukwuma Wilfred Onyema ya samu ƙuri’u 10,619, sai Arinze John Awogu a APGA ta zo ta uku da ƙuri’u 10,155.
Ta Kacame a Majalisar Dattawa Bayan Fara Kaɗa Kuri'a, An Yi Fafatawa Mai Zafi Tsakanin Akpabio da Yari
Mutum ɗaya 'yan jam'iyyar Labour za su marawa baya
Afam Ogene shi ne dai shugaban 'yan majalisa 35 da jam'iyyar Labour ke da su a majalisar wakilan.
A kwanakin baya, Vanguard ta wallafa cewa, 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar ta Labour sun sha alwashin zaɓar mutum ɗaya a yayin zaɓen kakakin majalisar wakilan ta goma.
Sun bayyana cewa zasu haɗu su duka su yi wa mutum ɗaya ruwan ƙuri'u, amma da sharaɗin cewa zai gamsar da su da manufofinsa.
Afam Ogene a yayin da yake jawabin, ya bayyana cewa duk da kowanensu na da ra'ayinsa na ƙashin kansa, za su marawa duk wanda suka gamsu da manufofinsa baya.
Akpabio ya ziyarci Tinubu a Villa
Legit.ng ta kawo muku rahoto kan ziyarar da sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya kai wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu jim kaɗan bayan rantsuwar kama aiki da ya yi.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Sanata Akpabio dai ya lashe zaɓen shugabancin majalisar ne bayan ya doke abokin gwabzawarsa, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar na jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng