Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

  • Godswill Akpabio ya yi galaba a kan Abdulaziz Yari wajen zama Shugaban Majalisar Dattawa
  • Sabon Shugaban Majalisar kasar ya fito daga Kudu maso kudu kamar yadda Jam’iyyar APC ta ke so
  • Sanata Akpabio ya tserewa tsohon Gwamna Abdulaziz Yari ne da ratar kuri’u 17 rak a zaben da aka yi

Abuja - Tsohon Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio ya lashe zaben majalisar dattawan Najeriya da aka yi a safiyar 13 ga watan Yuni 2023.

Dazu aka kammala tattara kuri’u a zaben shugaban majalisar dattawa da aka gudanar, kuma Sanata Godswill Akpabio ne wanda ya yi galaba.

Tsohon Gwamnan Zamfara ya tashi da kuri’u 46 kamar yadda Kilakin majalisa ya sanar da sakamakon jim kadan bayan an tattara kirgan kuri’u.

Godswill Akpabio
Lawan, Tinubu da Sabon Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yadda sakamakon zabe ya kasance

Shi kuma Sanata Godswill Akpabio ya samu Sanatoci 63 da su ka mara masa baya a takarar. Ratar kuri’u 17 ne tsakanin wadanda suka gwabza a zaben.

Kara karanta wannan

Ta Kacame a Majalisar Dattawa Bayan Fara Kaɗa Kuri'a, An Yi Fafatawa Mai Zafi Tsakanin Akpabio da Yari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duka Sanatoci 109 sun kada kuri’arsu a zaben, ba a samu ko daya da ya kauracewa jefa kuri’a ba. Akasin haka ya faru a lokacin zaben majalisa ta takwas.

Tsohon Gwamnan Akwa Ibom shi ne wanda tun farko ya samu goyon bayan jam’iyyar APC mai-ci ganin cewa shi Kirista ne daga kudancin Najeriya.

Kamar yadda bidiyon da aka haska kai-tsaye a shafin majalisa na dandalin Facebook ya nuna, ana kammala tattara sakamakon, Sanatoci su ka fara murna.

Da kyar Kilakin majalisar ya shawo kan majalisar dattawan domin sanar da sakamako. NTA ta tabbatar da wannan labari a shafinta na Twitter.

Magoya bayan Akpabio sai murna

Magoya baya sun je sun rungumi Godswill Akpabio domin taya sa murna. Hakan ya na nufin shi ne zai gaji Ahmad Lawan a majalisar tarayya ta goma.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalilai 5 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Legit.ng Hausa ta fahimci nasarar Akpabio ta na nufin Sanata mai wakilta Arewacin Kano a APC, Barau Jibrin zai zama mataimakin shugaban majalisa.

Yanzu kallo ya koma majalisar wakilan tarayya inda mutane 360 ne za su kada kuri’a a zaben.

Yadda aka tsaida 'yan takara

A baya an ji labarin yadda Sanata Ali Ndume daga Borno ta Kudu ya tsaida Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takaran shugaban majalisar dattawa.

Nan take shi kuma Sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya tsaida Abdulaziz Yari wanda zai wakilci Zamfara ta yamma, sai aka fara hayaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng