Bola Tinubu: Yan Najeriya Su Tsammaci Jerin Sunayen Ministocin Shugaban Kasa Daga Ranar Laraba
- Da kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu, Shugaban kasa Bola Tinubu ya kara karfin abubuwan da yan Najeriya ke tsammanin gani daga gwamnatinsa da wasu yunkuri da ya yi
- Yunkurin shugaban kasar ya sa yan Najeriya da dama zuba idanu don ganin su wanene za su kasance a jerin ministocinsa
- Sai dai kuma, yan Najeriya za su iya tsammanin ganin jerin ministocin Tinubu ne daga ranar 13 ga watan Yuni, lokacin da za a rantsar da majalisar dokoki ta 10
- Sai kuma ranar 28 ga watan Yuli, lokacin da shugaban kasar zai yi kwana 60 a ofis
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki wasu matakai tun daga rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, kuma hakan ya kara karfin abubuwan da yan Najeriya ke sa ran gani daga gwamnatinsa da yadda ya sanar da cire tallafin mai.
Biyo bayan rantsar da shi cikin abun da ya yi kasa da makonni 2, sabuwar gwamnatin shugaban kasa Tinubu ta yi wasu yunkuri da za a iya daukarsu a matsayin masu tsauri da nuna kishin kasa, kamar sanya hannu a kudirin wutar lantarki.
Yaushe Tinubu zai sakarwa yan Najeriya sunayen ministocinsa
Sai dai kuma, abu na gaba da yan Najeriya suke zuba idon gani daga shugaban kasar shine jerin sunayen ministocinsa, kuma ana sanya ran ganinsu daga ranar Laraba, 14 ga watan Yuni da kuma kwanaki 45 masu zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Koda dai wasu sun yi muhawara cewa ya kamata shugaban kasar ya saki sunayen ministocinsa a kan lokaci, wannan ba shine matsala ba domin ba zai iya aikata hakan ba tare da an rantsar da majalisar dokoki ta 10 ba.
Saboda haka, tunda ya zama dole sai jerin sunayen ministocin Tinubu ya bi ta majalisar tarayya kafin su amince da mambobin majalisarsa, ya kamata yan Najeriya su fara sa rai ga sunayen daga ranar Laraba, washegarin ranar da za a rantsar da majalisar.
Dalilin da zai sa yasa Tinubu ya saki jerin sunayen ministocinsa tsakanin watanni 2
Hakazalika, za a ci gaba da jiran tsammani tsakanin yanzu da kwanaki 45 masu zuwa. Hakan ya kasance ne saboda sabuwar dokar da ta wajabtawa sabon shugaban kasa da gwamnoni gabatar da jerin sunayen yan majalisunsu tsakanin kwanaki 60 da kama aikinsu.
Shugaban kasa Tinubu ya kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu kuma zai cike kwanaki 60 kan karagar mulki a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, wanda a tsakanin ne doka ta nemi ya gabatar da jerin sunayen ministocinsa.
Shugaban majalisar dattawa: Gwamnoni na tare da zabin shugaba Tinubu, Seyi Makinde
A wani labari na daban, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa shi da yan uwansa gwamnoni suna tare da dan takarar da shugaban kasa Bola Tinubu ke so ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba.
A ranar Talata, 13 ga watan Yuni ne za a rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 kuma a nan ne za a zabi wadanda za su jagoranci harkokin shugabanci a majalisar.
Asali: Legit.ng