'Ku Kiyayi Ganda, Tana Da Hadari A Yanzu', FG Ta Ankarar Da 'Yan Najeriya Game Da Barkewar Sabuwar Cuta

'Ku Kiyayi Ganda, Tana Da Hadari A Yanzu', FG Ta Ankarar Da 'Yan Najeriya Game Da Barkewar Sabuwar Cuta

  • Ma'aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya ta gargaɗi 'yan ƙasa game da ɓarkewar cutar Anthrax a wasu ƙasashen da ba su da nisa da Najeriya
  • Ma’aikatar ta shawarci ‘yan Najeriya da su guji cin ganda, naman da aka burara, da namun daji saboda haɗarin da ke tattare da su a yanzu har sai an shawo kan lamarin
  • Anthrax cuta ce da ka iya shafar dabbobi da mutane, kuma ana iya kamuwa da ita ta hanyar mu'amala da dabbobin da suke ɗauke da ita ko namansu

Abuja - Ma’aikatar Noma da Raya Karkara Ta Tarayya, ta sanar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar Anthrax a wasu ƙasashen yammacin Afrika da ke maƙwabtaka da Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Biyo bayan hakan, ma’aikatar ta shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin ganda, naman da aka burara (wanda aka bai wa tsoro da wuta), da namun daji saboda matukar haɗarinsu a yanzu har zuwa a shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Wani Abu Ya Fashe, Ya Kama da Wuta a Yankin Birnin Tarayya Abuja

Gwamnatin Tarayya ta gargadi 'yan Najeriya game da cin ganda
Gwamnatin tarayya ta ce a kiyayi cin ganda saboda hadarinta a yanzu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An samu bullar cutar Anthrax a Ghana, Togo da Burkina Faso

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma'aikatar, Dr Ernest Afolabi Umakhihe, ta ce an fara samun bullar cutar ta Anthrax ne a arewacin Ghana mai iyaka da Burkina Faso da Togo lamarin da ya jefa yankin cikin haɗari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Cutar wacce ta yi sanadin rasa rayuka, cuta ce da ke shafar dabbobi da mutane, wato cutar da za a iya ɗauka daga jikin dabbobi."
"Ana samun ƙwayoyin cutar ta Anthrax ne a cikin ƙasa, kuma galibi ta fi kama dabbobin gida da na daji."
“Mutane na iya kamuwa da cutar ta Anthrax idan suka yi mu’amala da dabbobin da suka kamu da cutar ko kuma gurbataccen naman dabbobin da ke ɗauke da ita.”

Sai dai kuma ya bayyana cewa, cutar ta Anthrax ba cuta ce mai yaɗuwa tsakanin mutum da mutum ba, saboda haka, ba za a iya kamuwa da ita ta hanyar kusanci da mai cutar ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Da Emefiele: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dakatar Da Gwamnan CBN

Ya ce:

“Alamomin Anthrax kamar na masassara ne, irinsu tari, zazzabi, da ciwon jiki, kuma idan ba a gano cutar da yin maganinta da wuri ba, ta na iya haifar da ciwon huhu matsananci, wahalar numfashi, firgici da kuma mutuwa.”

FG ta gargaɗi 'yan Najeriya kan kusanci da dabbobin da ke ɗauke da Anthrax

Sanarwar ta kuma gargaɗi jama’a game da kusanci da dabbobin da ba a yi musu allurar rigakafin cutar Anthrax ba, domin ana iya kamuwa da ita cikin sauki ta hanyar shakar kwayoyin cutar.

Daga cikin abubuwan da aka shawarci 'yan Najeriya su kiyaye, akwai cin naman dabbobi masu cutar, gandar da aka samu daga fatarsu, da kuma nonon da aka tatso daga garesu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnati ke fitar da irin gargadin ba, domin ko a shekarar 2022, The Guardian ta ruwaito cewa NAFDAC ta gargadi mazauna Legas kan cin naman gurbatacciyar ganda.

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

FG ta umarci bankuna su bai wa kwastomominsu katin ATM kyauta

A wani labarin Legit.ng ta wallafa a baya, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna hada-hadar kuɗi na 'yan kasuwa da su bai wa kwastomominsu sabon katin cirar kuɗi kyauta.

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin dijital a lokacin Buhari, Sheikh Isa Pantami ne ya bayyana haka a wajen wani taro a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng