Tsugunne Ba Ta Kare Ba, Bayan Da Kungiyar Arewa Ta Bukaci a Kama Ministan Buhari

Tsugunne Ba Ta Kare Ba, Bayan Da Kungiyar Arewa Ta Bukaci a Kama Ministan Buhari

  • Wata ƙungiyar 'yan Arewa CNF, ta yi kira da a kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a lokacin Buhari, Hadi Sirika tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa zarginsa da zamba
  • Ƙungiyar dai na zargin Hadi Sirika da zamba da kuma yaudarar 'yan Najeriya dangane da batun jirgin sama na Nigeria Air
  • Kiran na zuwa ne bayan kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama, ya bayyana batun na Nigeria Air a matsayin yaudara

Kaduna - Wata ƙungiyar rajin kare haƙƙin yan Arewa, CNF, ta yi kira da a kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a lokacin Buhari, Hadi Sirika tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa zarginsa da zamba kan batun Nigeria Air.

Kiran na zuwa ne bayan kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama, ya bayyana batun jirgin na 'Nigerian Air' a matsayin zamba.

Kara karanta wannan

Ashsha: Bata-Gari Sun Kone Gidan Rediyo Kurmus a Jihar Kogi, Sun Yi Wani Abu Kuma Daban

Kwamitin ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da kamfanin jirgin.

Kungiyar CNF ta nemi a kama Hadi Sirika
Kungiyar Arewa ta nemi a kama ministan Buhari, Hadi Sirika. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ƙungiya ta buƙaci a kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika

Ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis ta hannun shugabanta Ali Muhammad, ta buƙaci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), da ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muhammad ya ƙara da cewa, ministan ya yi abubuwa da dama ba tare da sauraro ko neman shawarar kowa ba. Ya ce hatta batun jirgin na Najeriya, bai saurari shawarar kowa ba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A kalamansa:

“Wannan abun kunya ne da almubazzarantar da dukiyar ƙasa, wanda za a iya hana faruwarsa inda ace ya saurari shawarar masana, amma kuma Sirika ya ƙaddamar da aikin duk da sanin cewa yaudara ce kawai da aka shiryawa ‘yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

Ƙungiyar ta ce shekaru takwas da Sirika ya yi duk yaudara ne

Kungiyar ta kuma ce, tsawon shekaru takwas da ya yi a matsayinsa na minista, babu abin da ya yi sai zamba da kuma yaudarar 'yan Najeriya.

A dalilin haka ne ƙungiyar ta yi kira ga Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), da ta tuhumi Hadi Sirika bisa abin da ta kira yaudarar 'yan Najeriya.

Vanguard ta ruwaito ƙungiyar na cewa Sirika ya kaddamar da jirgin duk da umarnin da kotu ta bayar kan cewa a dakatar da ƙaddamarwar.

Sirika ya ce jirgin Nigeria air zai fara tashi kafin Buhari ya sauka mulki

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ba da tabbaci cewa jirgin sama na Nigerian Air, zai fara tashi kafin Buhari ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Sirika ya bayyanawa manema labarai cewa an gama duk wasu shirye-shirye domin ganin jirgin ya fara aiki yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng