Cikakken Jerin Mata Mataimakan Gwamna a Najeriya Da Jihohinsu
Mata sun farga sun daina sanya akan harkokin siyasa a ƙasar nan, inda yanzu suke fitowa su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa.
Mata da dama sun riƙe muƙaman siyasa tun daga matakin kansila har ya zuwa na mataimakiyar gwamna.
Mun yi duba kan jerin matan da suka ɗare kujerar mataimakiyar gwamna a wannan zaɓen da ga gabata.
1. Monisade Afuye (Jihar Ekiti)
An haifeta a ranar 28 ga watan Satumban 1958, Monisade Afuye ita ce yanzu haka mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An haifeta ne a cikin gidan sarautar marigayi yarima Noah Afeni Adegboye da sarauniya Esther Adegboye.
2. Prof Ngozi Ordu (Jihar Rivers)
Farfesa Ngozi Ordu mai shekara 70 a duniya ta kai matsayin farfesa ne a jami'ar Port Harcourt.
Farfesar ta samu gogewa a harkar ilmi inda ake mata kallon ɗaya daga manyan waɗanda ake ji da su a jihar Rivers a ɓangaren ilmi.
3. Dr. Hadiza Balarabe (Jijar Kaduna)
Hadiza Balarabe likita ce kuma gogaggiyar ƴar siyasa wacce ta fito daga jihar Kaduna.
Ta riƙe muƙamin mataimakiyar gwamna a ƙarƙashin mulkin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Kuma yanzu ita ce mataimakiyar gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
4. Naimot Salako Ayodele (Jihar Ogun)
An haifeta a ranar, 8 ga watan Janairun 1966, Naimot Salako Ayodele ita ce ɗiyar farko a wajen marigayi farfesa Lateef Akinola Salako NNOM, CON, babban farfesa a fannin pharmacology da therapeutics.
Naimot mai shekara 57 ta fara ɗarewa kan kujerar mataimakiyar gwamna ne a shekara 2019, lokacin da aka rantsar da ita tare da gwamna Dapo Abiodun.
Da Ɗumi-ɗumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Sanatan Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ya Rasu A Asibitin Amurka
A ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, ta sake koma kan kujerar a karo na biyu tare da gwamna Abiodun.
5. Dr Akon Enyakenyi (Jihar Akwa Ibom)
Sanata Akon Enyakenyi, ta cimma nasara sosai a fannin siyasa tun kafin zamanta mataimakiyar gwamnan jihar Akwa Ibom.
Akon Enyakenyi ta yi aiki a gwamnatin tarayya a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
6. Josephine Piyo (Jihar Plateau)
Josephine Piyo ba baƙuwa bace a fannin siyasa domin ta daɗe ana damawa da ita a harkokin siyasa.
Ta riƙe muƙamai da yawa da suka haɗa da shugabar ƙaramar hukumar Riyom, ƴar majalisar dokokin jiha, mai bawa gwamna shawara ta musamman da ƴar majalisar wakilai.
7. Patricia Obila (Jihar Ebonyi)
Kafin ta zama mataimakiyar gwamna, Mrs Obila ta goge sosai kuma sananniyar ƴar siyasa ce a jihar Ebonyi.
Ta taɓa riƙe muƙamin shugabar ƙaramar hukumar Afikpo ta Arewa har sau biyu. Ita ce mataimakiyar gwamna mace ta farko da aka taɓa yi a jihar Ebonyi tun daga shekarar 1996.
8. Kaletapwa G. Farauta (Jihar Adamawa)
An haifi farfesa Kaletapwa G. Farauta a ranar 28 ga watan Nuwamba, 1965 a ƙaramar hukumar Numan.
Kafin zamanta mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa ta taɓa riƙe muƙamin kwamishina a jihar. Ta kuma riƙe shugabar riƙo ta jami'ar jihar Adamawa da ke Mubi.
Wike Ya Musanta Yin Magudi a Zaben Rivers
A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya musanta zargin cewa ya tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na jihar Rivers saboda Bola Tinubu ya yi nasara.
Wike ya musanta rahotannin binciken da ya tabbatar da cewa an yi wa shugaba Tinubu aringizon ƙuri'u a jihar Rivers.
Asali: Legit.ng