Hakeem Baba Ahmed Ya Caccaki Tikitin Muslim-Muslim, Ya Ce Yaudara Ce, Kuma Bai Amfani Musulman Ba

Hakeem Baba Ahmed Ya Caccaki Tikitin Muslim-Muslim, Ya Ce Yaudara Ce, Kuma Bai Amfani Musulman Ba

  • Dakta Hakeem Baba Ahmed, daraktan yaɗa labarai na kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a Kaduna yaudara ne
  • Ya bayyana cewa hakan bai amfani Musulmi da komai ba, tunda kaso 95 cikin 100 na gine-ginen da El-Rufai ya rushe a Kaduna na Musulmi ne
  • Ya kuma ce yan siyasa sun gurɓata harkar ta hanyar shigar da addini cikinta, inda ya yi kira ga 'yan Najeriya da su fahimci cewa babu wanda ke wakiltar wani addini

Daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba Ahmed, ya ce tikitin Musulim-Musulim yaudara ne.

Baba Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, a yayin da yake tsokaci game da zaɓin APC na ɗan takarar shugabancin majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

Hakeem Baba Ahmed ya caccaki batun Muslim Muslim
Hakeem Baba Ahmed ya ce tikitin Muslim-Muslim bai amfanawa Musulmai komai ba. Hoto: The Poise Nigeria
Asali: UGC

Baba Ahmed kan maganar zaɓen majalisa

Ya ce ya kamata a bar ‘yan majalisun su zaɓi wanda suke so ya jagorance su a zauren majalisar ta 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakeem Baba Ahmed ya kuma bayyana cewa ya kamata a bar yankin Arewa maso Yamma ya samar da shugaban majalisar dattawan, yana mai cewa kuri’unsu ne suka kawo Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki.

Hakeem kan batun Muslim-Muslim

Da yake tsokaci game da tikitin muslim-muslim a jihar Kaduna, Baba Ahmed ya bayyana cewa wannan ba komai ba ne face yaudara.

Ya ce babu abinda El-Rufai ya yi wa Musulmi in banda rusa musu gidajensu da ya yi. Ya ce kaso 95 cikin 100 na gine-ginen da aka rusa duk na musulmi ne.

A cewarsa:

“Me (El-Rufai) ya yi wa musulmi? Sai rusa musu gidaje. Kaso 95 cikin 100 na gidaje da gine-ginen da ya rushe duk na musulmi ne. To wane amfani muslim-muslim ta yi wa musulman? Yaudara ce kawai.”

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa Sun Cimma Matsaya, Sun Yanke Matakin da Zasu Ɗauka Kan Baiwa Yan Bindiga Kuɗi

Hakeem Baba Ahmed ya koka kan shigar da addini cikin siyasa

Hakeem Baba Ahmed ya koka kan yadda 'yan siyasa ke neman bata harkokin siyasar ƙasar nan ta hanyar shigo da addini cikinta.

Ya ƙara da cewa, yan siyasa sun gurɓata harkokin addini. Sun mayar da addinin wani makaminsu na siyasa, wanda suke wasa da hankulan mutane da shi.

Ya shawarci 'yan Najeriya kan su yi wa kansu karantun ta natsu, wajen fahimtar cewa babu wani ɗan siyasa da ke wakiltar wani addini, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Gwamnonin Arewa sun cimma matsaya kan yadda za su tunkari matsalar tsaro

A wani labarin da muka wallafa a baya, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya bayyana cewa sun yi zama, sun yanke shawara kan yadda za su ɓullowa matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Uba Sani ya ce, shi da sauran gwamnonin sun yi zama, sun yanke shawarar cewa ba za su bi hanyar bai wa 'yan bindiga kuɗaɗen fansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng