Sati Daya Bayan Hawa Mulki, An Bukaci Gwamnan Jihar Ebonyi Ƴa Yi Murabus

Sati Daya Bayan Hawa Mulki, An Bukaci Gwamnan Jihar Ebonyi Ƴa Yi Murabus

  • Sati ɗaya bayan kan madafun ikon jihar Ebonyi, gwamna Francis Ogbonna Nwifiru na cikin gagarumar matsala
  • Wata ƙungiyar ƴan asalin jihar mazauna ƙasar waje na neman dole ya tattara ƴan komatsansa ya yi murabus daga. Mulki
  • Ƙungiyar tace gwamnan ya kasa taɓuka komai sai abinda magabacinsa a sanya shi, alamun bai shirya ba kenan daga yin mulki

FCT, Abuja - Sati ɗaya bayan ya hau mulkin jihar Ebonyi, ƴan asalin jihar a ƙarƙashin ƙungiyar Association of Ebonyi Indigenes Socio-Cultural in the Diaspora (AEISCID), sun nemi gwamnan jihar Francis Ogbonna Nwifuru, da ya yi murabus.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƙungiyar ta ƴan asalin jihar mazauna ƙasashen waje, ta zargi gwamnan da kasa taɓuka komai sai abinda magabacinsa, Dave Umahi, ya sanya shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: INEC Ta Saki Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo

An nemi gwamnan Ebonyi da ya yi murabus
Kungiyar tace gwamnan ya kasa taɓuka komai Hoto: Francis Ogbonna Nwifiru
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 6 ga watan Yuni, shugaban ƙungiyar AEISCID, Pascal Oluchchukwu, ya ce gwamnatin bata nuna wata alamar mulki ba.

A cikin sanarwar, Oluchchukwu ya yi kira ga babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Usman Baba-Alkali, da ya janye ƴan sanda da aka ba gwamnan sannan ya buƙaci hukumomin yaƙi da cin hanci su cafke Umahi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Sati ɗaya bayan ya yi rantsuwar kama mulki, mun yi mamakin yadda har yanzu ƴan jihar Ebonyi basu ga wani ɓurɓushin alamar mulki ba, ko naɗin muƙarrabansa ya kasa yi.
"A maimakon hakan, mun yi ta karanta rahotanni cewa magabacinsa, Umahi, har yanzu yana zuwa duba wasu ayyuka waɗanda ba a kammala ba a jihar."

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan ya tashi haiƙan kan abinda ya kawo shi mulki

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ma'aikatan Shari'a Na Kasa Sun Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

Ƙungiyar ta AEISCID ta buƙaci gwamna Nwifuru da ya dawo cikin hayyacinsa ya kama ayyukan da suka rataya a wuyansa a maimakon ya riƙa bin umarnin abinda Umahi ya sanya shi.

A cewar rahoton Tribune, sanarwae ta ci gaba da cewa:

"Muna ƙalubalantar Nwifuru da ko dai ya kama mulki yadda yakamata kamar yadda takwarorinsa na jihohin Enugu da Abia suka fara, ko kuma ya yi murabus ya ba wanda ya san abinda mulki ya ƙunsa ya ci ɗora daga inda ya tsaya."

Kwanaki Kadan Da Barin Mulki, An Nemi a Binciki Gwamnatin Buhari

Rahoto ya zo kan yadda ƙungiyar SERAP ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya binciki ƙwangilolin tallafin mai da gwamnatin tarayya ta bada a mulkin Buhari.

SERAP na neman a yi bincike domin bin kadin yadda aka kashe kuɗin tallafin da aka bada daga 2016 zuwa 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel