Wike: Tsohon Gwamnan Ribas Ya Bayyana Dalilin Da Ya Kamata APC Ta Yi Godiya Ga Allah, Ya Kuma Caccaki PDP
- An bukaci ‘yan Najeriya da su taya gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da addu’a da kuma goyon baya
- Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ne ya yi wannan kira a garin Fatakwal na jihar Ribas
- Ya kuma ce ya kamata jam’iyya mai mulki ta godewa Allah saboda dama ta biyu da ta samu, tunda dai babu batun zargin da ake ma ta na musuluntar da Najeriya
Ribas, Fatakwal – Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce kamata ya yi gwamnatin APC mai mulki ta yi godiya da damar da ta samu a karo na biyu, duk da munanan ayyukan da suka yi wa ‘yan Najeriya.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata, 6 ga watan Yuni, yayin wata tattaunawa da manema labarai a garin Fatakwal na jihar Ribas.
A cikin hirar, Wike ya yi tsokaci kan manufofin shiyya-shiyya da jam’iyya mai mulki ta ɗauka. Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Wike yana cewa:
“Ya kamata APC su rika murna da cewa Allah ya ba su dama a kan PDP. Allah ya ba APC damar tuba daga laifukan da suka yi wa ’yan Najeriya.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya kuma caccaki jam’iyyarsa ta PDP kan rashin tsayawa kan tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar tun 1999.
Ya bayyana cewa dogaro da hasashen jam’iyyarsa ta PDP na samu wasu ƙuri'u ne ya janyo mata faɗuwa zaɓen shugaban ƙasa a watan Fabrairu.
Wike yayi magana akan batun Musuluntar da ƙasa da ake zargin Tinubu
Tsohon gwamnan na Ribas ya yabawa jam’iyyar APC kan yadda suka bi tsarin shiyya-shiyya, a yayin da kuma ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake na cewa shugaba Tinubu na da wata manufa ta Musuluntar da Najeriya.
Ku tuna cewa Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun fuskanci suka sosai saboda kasancewarsu 'yan addini ɗaya, domin ba a saba yin haka ba a tsarin shugancin Najeriya.
Wike ya buƙaci a yi wa Tinubu addu'a
A wani ɓangaren kuma, Wike ya ce jam’iyyar APC na da damar gyara kura-kuran da suka yi a baya.
A cewarsa:
"Allah ya ba su wannan damar a yanzu kuma suna son su yi watsi da ita ta hanyar rikice-rikicen cikin gida."
Wike ya bayyana cewa abin da Tinubu ke bukata a halin yanzu shi ne goyon baya da kuma addu’o’i daga ‘yan Najeriya, jaridar Independent ta ruwaito.
Wike ya ƙara da cewa idan shugaban ƙasa bai ji daɗin gudanar da mulki ba, akan 'yan ƙasa wahalar take ƙarewa, saboda haka ya shawarci kowane ɗan Najeriya ya yi abin da ya dace.
Kotu ta yi watsi da ƙarar da aka shigar da Tinubu
Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza
A wani labarin na daban, babbar Kotun Ta da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da aka shigar ta neman dakatar da rantsar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Wasu mutane biyar mazauna Abuja ne dai suka shigar da ƙarar a kwanakin baya, suna neman kotu ta dakatar da rantsar da Tinubu saboda a cewarsu bai samu kaso 25 cikin 100 na ƙuri'un FCT ba.
Asali: Legit.ng