Kotun Sauraren Kararrakin Zabe: Cikakken Jerin Jihohin Da Peter Obi Ke Kalubalantar Sakamakon INEC

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe: Cikakken Jerin Jihohin Da Peter Obi Ke Kalubalantar Sakamakon INEC

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, na ƙalubalantar sakamakon zaɓen jihohi aƙalla 20
  • Obi yana ganin cewa zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu cike yake da kura-kurai daban-daban da suka shafi ƙuri'un da aka kaɗa
  • Obi, wanda tsohon gwamnan Anambra ne, ya yi iƙirarin cewa akwai jihohi kusan 10 da aka hana wasu mutanen jefa ƙuri'unsu

Peter Obi, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar Labour, yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta fitar na ranar 25 ga watan Fabrairu.

A wata ƙara da ya gabatar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ranar Laraba, 22 ga watan Maris, Obi ya gabatar da hujjojin da yake taƙama da su.

Obi ya kalubalanci INEC kan zaben jihohi 20
Peter Obi ya ce an tafka magudi a jihohi 20 da ya gabatarwa kotu. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Obi ya ce an tafka maguɗi a zaɓen na 2023

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Obi ya ce zaɓen da ya samar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, cike yake da maguɗi, tauye masu kaɗa ƙuri'a, da rashin bin ka’idojin dokar zaɓe a jihohi daban-daban, in ji rahoton Premium Times.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihohin da Obi ke iƙirarin waɗannan abubuwan sun faru sune kamar haka:

  1. Rivers
  2. Legas
  3. Taraba
  4. Binuwai
  5. Adamawa
  6. Imo
  7. Bauchi
  8. Borno
  9. Kaduna
  10. Filato
  11. Ekiti
  12. Oyo
  13. Ondo
  14. Osun
  15. Kano
  16. Katsina
  17. Kwara
  18. Gombe
  19. Yobe
  20. Neja

Obi ya lissafo jihohin da aka tauye masu kaɗa kuri’a

Jihohin da tsohon gwamnan Anambra ya yi zargin cewa an aiwatar da ayyuka na tauye masu kaɗa kuri’a da dama, sune kamar haka:

  1. Borno
  2. Taraba
  3. Ekiti
  4. Oyo
  5. Ondo
  6. Taraba
  7. Osun
  8. Kano
  9. Katsina
  10. Kwara
  11. Gombe
  12. Yobe
  13. Neja

Business Day ta ruwaito cewa Peter Obi ya yi zargin cewa a cikin jihohin da aka lissafa a sama, bincikensa ya nuna masa cewa ƙuri’un da aka kaɗa a rumfunan zaɓe, sun zarce adadin masu kaɗa kuri’a da BVAS ta tantance a jihohin.

Kara karanta wannan

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

Bai kamata a ayyana Atiku ko Tinubu ba a matsayin shugaban ƙasa, cewar shaidan PDP

A baya, Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan wani daga cikin shaidun da ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar a gaban kotu, da ya fito ya shaidawa kotun cewa Atiku da Tinubu ba su cancanci zama shugaban ƙasa ba.

Mutumin ya dogara ne da cewa dokar ƙasa ta tanadi cewa dole ne ya kasance ɗan takara ya samu aƙalla kaso 25 cikin 100 na ƙuri'un FCT da aka kaɗa, kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng