Matatar Dangote ba za ta Jawo Farashin Fetur Ya Yi Sauki ba Inji Shugaban NNPCL
- Da aka zanta da shi, Mele Kolo Kyari ya nuna babu tabbacin litar man fetur za tayi araha nan kusa
- Wasu su na cewa da zarar Aliko Dangote ya fara tace danyen mai, mutane za su saye fetur da sauki
- Shugaban NNPCL ya ce ko da matatar Dangote ko wata matata ta na aiki, farashi ba zai canza ba
Abuja - Ko zuwa lokacin da matatar kamfanin Dangote da sauran matatun danyen mai za su soma aiki a Najeriya, farashin man fetur ba zai sauka ba.
Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari ne a lokacin da ya yi hira da gidan talabijin Arise TV a yammacin Alhamis.
Malam Mele Kolo Kyari ya fito karara yake cewa batun a ce farashin litar mai zai sauka da zarar an fara samun fetur a kasar nan sam ba gaskiya ba ne.
A hirar da aka yi da shi, Mele Kyari ya tabbatar da cewa daga karshen Yuli zuwa Agusta, matatar Dangote da aka kaddamar za ta soma cire man fetur.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi nisa wajen gyara wata matatar mai, kuma ana sa nan da 2025 sauran matatun duk su fara samar da fetur, amma hakan bai nufin farashi zai sauka.
Za a gamu da cikas
Kyari ya amince cewa matakin da aka dauka na janye tsarin tallafin man fetur zai zo da irin na sa matsalolin, daga ciki shi ne zai haddasa tsadar kaya.
Shugaban kamfanin man kasar ya ce daga yanzu farashin litar fetur ya danganta ne da abin da ‘yan kasuwa su ka tsaida, su ne ke da wuka da nama.
A cewar Kyari, har a kasashen da aka cigaba a Duniya, a kan yi fama da matsaloli na hauhawar farashin idan aka shiga matsin lambar tattalin arziki.
Motsa tattalin arziki
Punch ta rahoto Malam Kyari ya na cewa abin da sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ya ke so shi ne tattalin arzikin Najeriya ya motsa da 7% a shekara.
Shugaban kamfanin na NNPCL ya na ganin abubuwa za su dawo daidai bayan janye tallafin man fetur.
Kamar yadda bayanin da Kyari ya yi ya nuna, 38% na duka man fetur da ake sha a Najeriya su na karewa ne a Abuja, Legas, Fatakwal da kuma Kano.
Za a kawo tsare-tsare
Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari ya shaida cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umarni a samar da tsare-tsare a dalilin cire tallafin ma.
Sai da ta kai a duk wata Najeriya ta na kashe Naira Biliyan 400 a wajen biyan tallafin fetur, Kyari ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da batar da biliyoyi ba.
Asali: Legit.ng