Gwamnonin Najeriya 3 Da Ke Amfani Da Motocin Da Aka Kera a Najeriya a Matsayin Motocinsu Na Hawa
Kamar yadda ake ganin cewa al'adace ta mafi yawa daga cikin 'yan Najeriya, wajen fifita kayayyakin da aka siyo a ƙasashen waje a kan waɗanda aka yi a nan cikin gida.
Har yanzu akan samu wasu 'yan ƙasa masu kishi da ke daraja kayayyakin gida fiye da na ƙasashen waje, musamman ma dai idan ya kasance na gidan suna da inganci.
Daga cikin irin waɗannan 'yan Najeriyan, akwai wasu gwamnoni da ke amfani da motocin da aka ƙera a gida Najeriya a matsayin motocinsu na ofis.
Jaridar Tribune Online ta binciko wasu gwamnonin Najeriya guda uku da ke amfani da motocin da aka ƙera a cikin gida a matsayin motocinsu na aiki, gwamnonin sune kamar haka:
1. Alex Otti
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alex Otti shine sabon gwamnan jihar Abia da ya karɓi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu da ta gabata.
An haifi Alex Otti a ranar 18 ga watan Fabrairu, 1965. Shi ne gwamnan jihar Abia na biyar tun dawowar Najeriya bisa tafarkin dimokuradiyya.
Alex Otti ɗaya ne daga cikin gwamnonin Najeriya ƙalilan da ke amfani da motocin da aka ƙera a cikin gida a matsayin motocin hawa da na ofis.
A wajen bikin ƙaddamar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, an hango Otti a kan mota ƙirar kamfanin motoci na Innoson.
2. Charles Soludo
An haifi Charles Soludo a ranar 28 ga Yuli, shekarar 1960. Ya fito ne daga ƙaramar hukumar Aguata, da ke jihar ta Anambra.
Soludo shi ne mutum na biyu a cikin jerin gwamnonin Najeriya da suke amfani da motocin da aka ƙera a Najeriya a matsayin motocin hawa ko na ofis.
3. Inuwa Yahaya
Shi ma Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya samu damar komawa kan kujerarsa a karo na biyu, inda aka sake rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Kamar takwaransa na jihar Abia, Gwamna Inuwa Yahaya shi ma ya yi amfani da mota ƙirar kamfanin motoci na Innoson a lokacin da aka rantsar da shi a filin wasa na Pantami.
Gwamnan Kwara ya gargaɗi 'yan kasuwar man fetur a jiharsa
A wani labarinmu na baya, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ja kunnen 'yan kasuwar man fetur na jihar da su guji jefa talakawa cikin mawuyacin halin rayuwa.
AbdulRahman, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, ya bayyana hakan ne ta hannun sakataren watsa labaransa Rafiu Ajakaye.
Asali: Legit.ng