Gwamnoni 4 Da Ke Ta Hankoron Kaddamar Da Ayyuka Gabanin Mika Mulki Gabanin Ranar 29 Ga Watan Mayu

Gwamnoni 4 Da Ke Ta Hankoron Kaddamar Da Ayyuka Gabanin Mika Mulki Gabanin Ranar 29 Ga Watan Mayu

Gabanin rantsar da shugaban ƙasa da sabbin gwamnatocin jihohi, wasu gwamnoni masu barin gado na ta hanƙoron ƙaddamar da ayyukan da suka yi, ciki kuwa hadda waɗanda basu ma kammala ba.

Hakan dai ana ganin yana da nasaba da irin rashin kyakkyawar alaka da wasu daga cikin gwamnonin ke da ita tsakaninsu da masu jiran gadon.

Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu gwamnoni guda huɗu da ke ta ƙoƙarin ƙaddamar da duka ayyukan da suka fara a jihohinsu gabanin miƙa mulki ga zaɓaɓɓun gwamnoni masu jiran gado.

Gwamnonin da ke kaddamar da ayyukan da basu kammala ba
Wasu gwamnoni na ta kaddamar da ayyuka gabanin mika mulki. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Darius Ishaku na Jihar Taraba

Gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishaku na sahun gaba cikin gwamnonin da ke ta yunƙurin ganin sun ƙaddamar da duka ayyukansu kafin miƙa mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bi Dare Sun Kai Mummunan Hari a Kaduna, Sun Sace Mutane Da Dama

An ce a cikin 'yan kwanakin nan, Darius ya ƙaddamar da ayyuka na biliyoyin nairori gabanin miƙawa zaɓaɓɓen gwamna, kuma mai jiran gado, Agbu Kefas.

Daga cikin ayyukan da ya ƙaddamar, akwai wata gada a yankin Pantisawa wacce ba a kammala ba.

Haka nan gwamnan ya ƙaddamar da rukunin wasu gidaje 500, da ya sanyawa suna ’Rukunin gidaje na Darius Dickson Ishaku', da ke kan hanyar Mutum Biyu cikin garin Jalingo.

An fara ayyukan gidajen ne tun a shekarar 2017, sai dai gwamnan ya ƙaddamar da su duk da cewa ba a kammala aikin kusan duka gidajen ba.

Abdullahi Ganduje na Jihar Kano

Haka nan na, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da ayyuka da dama gabanin miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamna wato Abba Kabir Yusuf.

Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar akwai waɗanda ba a kammala su ba, irinsu aikin titin Ahmadu Bello da kuma aikin ma'aikatar samar da wutar lantarki ta Tiga.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Rusa Majalisar Kwamishinoninsa, Ya Sallami Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa

Wani mamba a jam'iyyar NNPP, Ambasada Baba Bage, ya bayyana cewa ƙaddamar da ayyukan da ba a kammala ba, asarar kuɗin gwamnati ne kawai.

Samuel Ortom na Jihar Benue

A jihar Benuwai ma, gwamnan jihar mai barin gado, Samuel Ioraer Ortom, ya ƙaddamar da ayyuka da dama a sati biyu da suka gabata gabanin miƙawa zaɓaɓɓen gwamna Rabaran Hyacinth Alia na APC.

An ce gwamnan ya ƙaddamar da ayyuka da dama a ɗan ƙanƙanin lokaci a cikin birane da ƙauyukan jihar ta Benuwai.

Gwamnan ya umarci kwamishinoninsa da su ƙaddamar da duka ayyukan da ke yankunansu a madadinsa.

Haka nan kuma, Gwamna Ortom ya assasa wasu ayyukan na daban, waɗanda ya ce gwamnati mai zuwa ce za ta ƙarisa su.

Sai dai gwamnan na shan suka dangane da hakan musamman ma daga mambobin jam'iyyun adawa a jihar.

Ben Ayade na Jihar Kuros Ribas

A jihar Kuros Ribas ma, gwamna mai barin gado Benedict Bengiuoshuye Ayade, ya ƙaddamar da wasu ayyuka yana gab da zai miƙawa zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado Bassey Edet Otu mulkin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Ƙaddamar Da Bincike Kan Gwamnoni 28 Da Mataimakansu Gabanin 29 Ga Watan Mayu

Gwamnan a cikin 'yan kwanakin nan ya ƙaddamar da ayyukan tagwayen hanyoyi da yayi a sassa daban-daban na jihar ta Kuros Riba.

Daga ciki akwai hanyar da ta tashi daga Calabar ta bi ta Odukpani zuwa Tinapa. Sannan kuma akwai gadar sama da gwamnan ya sanyawa suna 'Sphagetti da ya yi a hanyar Odukpani cikin birnin Calabar, wacce ita ma ba a kammala ba.

Haka nan kuma an ce akwai makaranta da asibiti dama wasu ayyuka da dama da gwamnan ya ƙaddamar ba tare da an kammala su ba.

EFCC za ta binciki gwamnoni 28

A wani labarin da muka wallafa a baya, kun karanta cewa hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta ƙaddamar da bincike akan gwamnoni guda 28.

Daga cikin gwamnonin da EFCC za ta bincika akwai waɗanda za su koma a zagaye na biyu, wasunsu kuma sun kammala, a yayin da wasu kuma iya zagaye na ɗaya kawai suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel