Sabon Gwamnan Sokoto Ya Sha Alwashin Kwato Kadarorin Gwamnatin Jihar Da Aka Siyar
- Sabon gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya ɗauki alƙwarin ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da gwamnan da ya gada ya rabar a jihar
- Gwamnan ya sha alwashin ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin kadarorin da aka yi baje kolinsu ya ƙwato su
- Ahmed Aliyu ya bayyana cewa duk wanda bai dawo da kadarorin ta lalama ba, zai dawo da su ko da kuwa da ƙarfin tuwo ne
Jihar Sokoto - Sabon gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya sha alwashin ƙwato dukkanin kadarorin gwamnati da wasu tsiraru suka siya a lokacin mulkin gwamnatin da ya gada.
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wata liyafa, da aka shirya domin tarbarsa da shi da mataimakinsa, Idris Gobir, a daren ranar Litinin.
Gwamnan ya bayyana cewa kadarorin jihar mallakin al'ummar jihar ne, ba wai na wani daban ba wanda zai siyar ko ya rabar da su, ba tare da bin hanyar da ta dace ba.
Gwamnan ya kuma buƙaci duk wanda ya san ya amfana daga irin wannan rabon da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta yi, da ya gaggauta dawo da waɗannan kadarorin hannun gwamnati ko kuma a tilasta masa yin hakan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"A lokacin yaƙin neman zaɓe na, na yi alƙawarin ba zanci amanar al'ummar jihar nan ba ko in bari wani ya ci amanar su. Na yi alƙawarin kare mutanen jihar nan da dukiyoyin su, kuma ba zan kasance cikin masu raba kadarorin jihar nan ba ga ƴan barandarsu"
"Ina son na yi amfani da wannan damar ga duk wanda ya san ya amfana daga waɗannan kadarorin, ko da ɗan jam'iyyata ta APC ne ko jam'iyyar PDP, da ya dawo da su ko kuma a tilasta masa yin hakan."
Gwamnan ya ce ya sauya daga yadda aka san shi a baya
Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa ya sauya daga sanin da aka yi masa a baya na mai neman gwamnan jihar.
"Ahmed Aliyun da kuka sani a lokacin yaƙin neman zaɓe ya banbanta da wanda ya ke gwamna yanzu. Yanzu nine gwamnan jiha, dukkanin alhaƙin al'ummar jihar nan ya rataya a wuya na." A cewarsa.
"Duk wanda ya ƙi ya dawo da waɗannan kadarorin zai fuskanci fushin hukuma."
Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Kwato Kadarorin Da Ganduje Ya Siyar
A wani rahoton na daban kuma, sabon gwamnan jihar Kano, ya sha alwashin kwato kadarorin da Ganduje ya siyar a jihar.
Abba Kabir Yusuf ya kuma sauke dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da ke jagorantar hukumomin gwamnati a jihar.
Asali: Legit.ng