Zan Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira da Buhari Ya Yi, Shugaba Tinubu

Zan Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira da Buhari Ya Yi, Shugaba Tinubu

  • Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai sake nazari kan tsarin Buhari na sauya fasalin N200, N500 da N1000
  • Tinubu ya faɗi haka ne a cikin jawabinsa na bikin rantsarwa wanda ya gudana a Eagle Square ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023
  • Ya ce babban bankin Najeriya ya tsaurara wa mutane bisa kawo tsarin duba da yawan waɗanda ba su da asusun banki

Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata sake nazari kan tsarin sauya fasalin naira wanda magabacinsa ya aiwatar.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a cikin jawabinsa na wurin bikin rantsarwa a filin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Bola Tinubu.
Zan Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira da Buhari Ya Yi, Shugaba Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sabon shugaban kasan ya ce tsoffi da sabbin takardun naira za su ci gaba da zama halastattun kuɗi a hannunn 'yan Najeriya karkashin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Babu Sa'a: Mutane Sun Fadi Ra'ayinsu Yayin Da Ruwan Sama Ya Cika Inda Tinubu Zai Karbi Rantsuwa

Tinubu ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya zama wajibi babban bankin Najeriya ya daidaita farashin musayar kuɗi. Wannan zai sauya akalae kuɗi daga hannun 'yan canji zuwa zuba hannun jari mai amfani, kayayyaki da ayyukan da zasu bunƙasa tattalin arziki."
"Muna buƙatar rage kuɗin ruwa domin ƙara yawan zuba hannun jari da sayen kayayyaki ta hanyar da tattalin aiziƙin mu zai habaka."
"CBN ya tsaurara wa mutane, koma wace irin manufa ce, tsarin sauya fasalin naira ya ƙara jefa talaka cikin ƙunci musamman idan aka yi la'akari da yawan waɗanda ba su da asusun banki a ƙasar nan."

"Ya kamata mu sake nazari kan wannan tsari, amma a halin yanzu gwamnati na ta sahalewa 'yan Najeriya su ci gaba da amfani da duka tsoho da sabo takardun naira," inji shi.

Shugaba Tinubu ya gaji tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda wa'adinsa ya ƙare ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Bikin Rantsar Da Tinubu: Shehu Sani Ya Yi Hasashen Abinda Zai Faru Da Emefiele Bayan Saukar Buhari

Malami, Emefiele Da Wasu Yan Majalisar Buhari Da Za a Ji Su Shiru Da Zaran Tinubu Ya Karbi Mulki

A wani rahoton na daban kuma Mun haɗa muku masu faɗa a ji a gwamnatin Buhari da ba zasu shiga gwamnatin Bola Tinubu ba.

Mambobin majalisar zatarwan Buhari da suka hada da ministoci da sauran masu rike da mukamai na iya rasa shahararsu bayan mika mulki saboda irin baƙin fentin da suka shafa wa kansu a lokacin suna mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262