Tsohuwar ‘Yar Takarar Shugaban Kasa Ta Shaidawa Tinubu Kujerar da Take So a Mulkinsa
- Ibinabo Dokubo ta na so a duba sadaukarwa da tayi, ta hakura da neman zama ‘yar takara a APC
- ‘Yar siyasar ta ce kyau Bola Ahmed Tinubu ya saka mata da zama Minista idan ya dare kan mulki
- Idan za a dauko Ministan da zai wakilci jihar Ribas, Dokubo ta na so akalla tayi uwa da makarbiya
Abuja - Tsohuwar mai neman zama ‘yar takarar shugaban Najeriya, Ibinabo Dokubo, ta roki Bola Ahmed Tinubu ya ba ta kujerar Minista a gwamnatinsa.
A makon nan Premium Times ta rahoto Ibinabo Dokubo ta na mai cewa ta cancanci samun matsayi a gwamnati saboda hakura da tayi da neman takara.
Dokubo ta zanta da manema labarai a garin Abuja, ta tunawa Duniya lokacin da ta janye takararta saboda Tinubu ya yi nasara, kuma hakan dai aka yi.
‘Yar siyasar ta ce ta dace da zama Minista domin ta na da basirar da za ta iya taimakawa sabuwar gwamnatin da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Ibinabo Dokubo
"Ba wai na cancanci Minista kurum ba. Na dace da zama Ministar matasa, kuma a matsayin jagora a jam’iyyar APC ta jihar Ribas, zan iya sauke nauyin.
Ina da abin da zan kawowa gwamnati. Ina da muradu da-dama a lokacin da na tsaya neman tikitin takarar shugabancin kasa. Na cancanci Minista.
The Cable ta ce Ms Dokubo ta soki Gwamna Nyesom Wike mai barin-gado, ta zarge shi da lallabar Bola Tinubu da APC, ya na neman a ba shi wani mukami.
Ba cewa nake yi dole sai na zama Minista ba, amma dole in zama cikin tafiyar. Ko in zama, ko in kawo wani. Asiwaju ya ce gwamnatinsa ta matasa ce.
A kowane ma’auni aka dauka, na dace da zama Minista.
An yi wa Wike kaca-kaca
"Ina ganin Nyesom Wike ya na bin Asiwaju da APC. Wannan ita ce jam’iyyar da ya taba kira da kansa. Wike ya na so ya zama Minista a mulkin cutar daji?
- Ibinabo Dokubo
Nan da kusan awa 24, Bola Tinubu ne shugaban tarayyar Najeriya, dukkanin iko zai koma hannun sa, an ji labari mutane su na jiran nadin mukamai.
Mukaman da ake sauraro su ne masu magana da bakin shugaban kasa, shugaban ma’aikatan fadar Aso Rock Villa sai sakataren gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng