Abu 3 Da Kotun Koli Ta Yi La'akari Da Su Wajen Korar Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

Abu 3 Da Kotun Koli Ta Yi La'akari Da Su Wajen Korar Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

  • Bola Tinubu da Kashim Shettima sun kayar da jam’iyyar PDP a ƙarar da ta shigar ta neman soke takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da suka yi
  • Kotun koli a hukuncin da ta yanke ranar Juma’a, ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar kan batun takara biyu da suka zargi Shettima da yi
  • A hukuncin da kwamitin mutane 5 na kotun koli ya yanke, mai shari’a Adamu Jauro ya bayar da hujjoji 3 na doka da kuma kundin tsarin mulki domin tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke

Abuja - Kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar, tana neman a soke takarar da Bola Tinubu da Kashim Shettima suka yi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Ba Gudu Ba Ja Da Baya," Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙoli

PDP dai na ƙalubalantar tikitin takara biyu da suke zargin Shettima da shi da nufin dakatar da bikin rantsar da Tinubu da Shettiman a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a matsayin shugaban Najeriya da mataimakinsa da aka shirya gabatarwa.

Abubuwa uku da kotu ta lura da su wajen korar karar PDP a kan Tinubu
Abubuwa uku da kotu ta lura da su wajen korar karar PDP a kan Tinubu. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai shari’a Inyang Okoro ne ya jagoranci kwamitin mutane 5 na kotun ƙolin da ta yi watsi da ƙarar a ranar Juma’a, 26 ga watan Mayu.

Da yake karanto hukuncin kotun, mai shari’a Adamu Jauro, mamba a kwamitin shari'ar, ya sanar da korar ƙarar, inda ya bayar da wasu manyan dalilai guda 3 da kotun ta yi la'akari da su. Dalilan sune:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. PDP ba ta da hurumin shigar da ƙara kan harkokin cikin gidan APC

Kotun ta bayyana cewa PDP ba ta da hurumin ƙalubalantar al’amuran cikin gida na APC. Kotun kolin ta ambaci sashe na 285 (14) (c) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) da kuma sashe na 149 na dokar zaɓe ta 2022.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Dakatar da Rantsar da Bola Tinubu

A cewar Jauro:

"Babu wata jam'iyya da za ta iya ƙalubalantar zaben wata jam'iyyar."

Ya kuma ƙara da cewa babu wata jam’iyya da za ta iya ƙalubalantar ayyukan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) kan batun zaɓen ‘yan takara a wata jam’iyyar.

2. PDP ta kasa nuna illar da zaɓen Shettima ya janyo mata

Hukuncin ya ƙara da cewa ko kaɗan babu inda tikitin na Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu ya shafi PDP.

Jauro ya ci-gaba da cewa, PDP ta gaza fahimtar inda kotun ɗaukaka ƙara ta tantance manyan batutuwan da suka shafi ingancin shari’ar.

3. Ƙarar ta PDP makararriya ce

Wannan yana nufin cewa tun farko bai ma kamata a shigar da ƙarar ba, saboda matsayin doka a bayyane yake.

Kasancewar ƙarar ta PDP ta zo a makare ne babban dalilin da ya sa kotun daukaka ƙara a baya ta ci tarar PDP naira miliyan biyar (N5m), amma jam’iyyar ba ta gamsu ba sai ta ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli.

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

Yadda Tinubu ya yi amfani da Obi don kayar da Atiku

A wani labari na daban kuma, an zargi Tinubu da yin amfani da ɗan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi, wajen hana ɗan takarar PDP Atiku Abubakar yin nasara a zaɓen da ya gabata.

Ɗan takarar gwamna a jihar Oyo ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Tawfiq Akinwale ne ya yi wannan zargi a yayin hira da wani gidan radiyo a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng