Kungiya Ta Gabatarwa Tinubu Aikin Farko Da Ta Ke Son Ya Yi Da Zarar Ya Shiga Ofis

Kungiya Ta Gabatarwa Tinubu Aikin Farko Da Ta Ke Son Ya Yi Da Zarar Ya Shiga Ofis

  • Wata ƙungiyar rajin kare haƙƙin dimokuraɗiyya mai suna 'Rere Foundation' ta roƙi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi ƙoƙarin rage tsadar man fetur in aka rantsar da shi
  • Shugaban ƙungiyar Segun Adesanya ne ya yi kiran jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa farashin man ke sabbaba hauhawar farashin kayayyaki
  • Ya kuma kirayi zaɓaɓɓen shugaban kan ya sanya ido wajen tabbatar da ingancin kayayyakin masarufi da ake samarwa daga kamfanoni a ƙasar nan

Wata ƙungiya mai rajin kare dimokuraɗiyya, 'Rere Foundation' ta buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da ya yi ƙoƙari wajen ganin ya rage tsadar man fetur a lokacin da ya hau karagar mulki.

Ƙungiyar dai ta koka kan yadda tsadar man fetur ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki wanda hakan ke jefa rayuwar talakawan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Bai Kamata A Rantsar Da Tinubu A Ranar 29 Ga Watan Mayu Ba, Datti Baba-Ahmed Ya Bayani

An nemi Tinubu ya rage farashin mai a Najeriya bayan ya karbi mulki
An nemi Tinubu ya rage farashin mai a Najeriya bayan ya karbi mulki. Hoto: Punch
Asali: UGC

Rage farashin zai rage raɗaɗin da ake ciki

Kamar yadda Punch ta ruwaito, shugaban ƙungiyar, Segun Adesanya a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa rage tsadar man fetur za ta rage raɗaɗin da ‘yan Najeriya ke ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adesanya, ya buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da ya tabbatar da an samu faduwar farashi tsakanin naira da dala da ma sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

Ya jaddada cewa akwai buƙatar Tinubu ya magance matsalolin abubuwan da ke kawo tasgaro wajen samun ayyukan yi a ƙasa.

Akwai buƙatar Tinubu ya kula da ingancin kayan masarufi

Sannan ya ƙara da cewa akwai buƙatar Tinubu ya tabbatar da ingancin kayayyakin masarufi da kamfanoni masu zaman kansu da ma na gwamnati ke samarwa a ƙasar nan.

Ya koka kan yadda yake tunanin cewa hukumomin da ke da alhakin lura da ingancin kayayyaki ba sa yin abinda ya kamata wajen tabbatar da ingancinsu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

A kalamansa:

“Ya kamata zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya tabbatar da ingancin mafi akasarin kayayyaki da kuma ayyukan da kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati ke yi a Najeriya.”
“Akwai kayayyaki marasa inganci da yawa a fadin kasar nan. Hukumar SON, NAFDAC da dai sauransu da alama ba sa yin abinda ya kamata sosai a 'yan kwanakin nan kuma babu wanda ya damu da hakan.”

Buhari ya faɗawa Tinubu kalamai masu kyawu

A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya bayyana cewa yana da kyakkyawan zato cewa Najeriya za ta ci-gaba da ɓunƙasa a ƙarƙashin mulkin Tinubu.

Buhari ya yi kalaman ne a wajen bikin bayar da lambar girmamawa ta GCFR ga Tinubu a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng