Tinubu Ya Yi Wa Obasanjo Wankin Babban Bargo, Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu Da Ya Kasa Yi Wanda Buhari Ya Yi

Tinubu Ya Yi Wa Obasanjo Wankin Babban Bargo, Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu Da Ya Kasa Yi Wanda Buhari Ya Yi

  • Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yabawa shugaba Buhari bisa mayar da ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar dimokuraɗiyya
  • Tinubu ya yi wannan yabawar ne yayin da ya ke yin shagube ga tsaffin shugabannin ƙasar nan, Olusegun Obasanjo, Umar Yar'Adua da Jonathan
  • Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin 'Mr Democrat' yayin da ya ke yaba masa bisa karrama shi da babbar lambar yabo ta ƙasa ta GCFR

Abuja - Bola Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ya yi wa tsaffin shugabannin ƙasar nan, Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar'Adua, Goodluck Jonathan, shagube bisa gazawarsu wajen tunawa da zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993 da wanda ya lashe zaɓen Cif MKO Abiola.

Tinubu ya kuma yabawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bisa tunawa da Abiola da zaɓen ranar 12 ga watan Yuni, inda ya bayyana shugaban ƙasar mai barin gado a matsayin "Mr. Democrat".

Kara karanta wannan

"Najeriya Zata Ƙara Bunkasa," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Tinubu Wasu Kalamai Masu Kyau

Bola Tinubu ya yabawa shugaba Buhari
Tinubu ya ce shugaba Buhari ya yi abinda Obasanjo ya gaza yi Hoto: Punch.com
Asali: UGC

A cewar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, shugaba Buhari ya kafa tarihi sannan babu wanda ya isa ya musanta gudunmawar da bayar wajen ci gaban ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa gudunmawar da ya bayar ta fi ta Obasanjo da sauran tsaffin shugabannin ƙasar nan.

Tinubu ya yaba da karrama Abiola da Buhari ya yi

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Shugaba Buhari, ka nuna ƙwarin guiwa sannan ka yi hukunce-hukunce masu tsauri waɗanda wasu suka kasa yi. Ɗaya daga cikinsu shine tunawa da rashin adalcin da aka yi na soke zaɓen 1993, da mayar da ranar 12 ga watan Yuni ranar dimokuraɗiyya sannan da karrama Cif MKO Abiola da babbar lambar yabo ta ƙasa."
"Kamar yadda yakamata kowa ya yi, ka tuna da tarihi domin warkar da raunin da aka yi a baya."

Tinubu ya dai yi wannan furucin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayun 2023, bayan ya karɓi lambar yabo ta GCFR daga hannun shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Najeriya Zata Ƙara Bunkasa a Mulkin Bola Tinubu, Shugaba Buhari

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi wa ƴan Najeriya wani muhimmin albishir.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya za ta bunƙasa matuƙa a mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng