Amurka Ta Zabi Jami’an Gwamnati 9 da Za Su Halarci Bikin Rantsar da Tinubu a Abuja
- Kasar Amurka ta fara shirye-shiryen halartar bikin rantsuwar sabon shugaban kasa da za ayi a Najeriya
- Joseph R. Biden Jr. ya turo wakilai a karkashin jagorancin Misis Marcia L. Fudge zuwa birnin tarayya Abuja
- Tawagar ta kunshi Janar Michael E. Langley da Mary Catherine Phee da kuma wasu kusoshin Gwamnati
Washington - Shugaban kasar Amurka, Joseph R. Biden Jr. ya zabi tawagar da za ta zo Najeriya wajen rantsar da sabon shugaban kasa da za ayi.
Wani jawabi da ya fito daga fadar White House ya tabbatar da cewa Mista Joseph R. Biden Jr zai turo wakilai zuwa garin Abuja a mako mai zuwa.
A ranar 29 ga watan Mayu ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai canji Muhammadu Buhari, shugabannin kasashen Duniya da-dama za su halarci taron.
Sanarwar da aka fitar a ranar Litinin ya nuna Ministar ayyuka da raye birane, Marcia L. Fudge za ta jagoranci tawagar da za ta wakilci Joe Biden.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ce sauran ‘yan tawagar sun hada da Jakadu a manyan jami’an Amurka.
Biden ya ware mutane tara su wakilce shi a taron da za ayi. Darektar hukumar cigaban kasuwancin Amurka, Enoh T. Ebong ta na cikin tawagar.
Ragowar ‘yan tawagar
- Mista David Greene – Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja
- Mai girma Sydney Kamlager-Dove – Wakilin Amurka a Kalifoniya
- Mai girma Marisa Lago – Karkashin ma’aikatar kasuwancin Amurka
- Janar Michael E. Langley – Kwamandan Dakarun Afrika na Amurka
- Mai girma Enoh T. Ebong – Darektar hukumar cigaban kasuwancin Amurka
- Mai girma Mary Catherine Phee – Karamar Ministar harkokin Afrika.
- Judd Devermont – Babban mai ba Shugaban kasa shawara kuma Darekta a hukumar kula da harkokin Afrika da NSC
- Mai girma Monde Muyangwa – Jami’i a hukumar harkokin Afrika da USAID.
Kudirori sun zama doka
An ji labari Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mai barin gadon mulki ya rattaba hannu a kan dokokin da za su bunkasa karatu da bincike a kasa.
Dokar kasa ta tabbatar da kafuwar jami’o’in kiwon lafiya a garuruwan Ila-Orangun da Azare da hukumar NSIP domin inganta rayuwar marasa galihu.
Asali: Legit.ng