Sabuwar Rigima Za Ta Barke Tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike a Jam’iyyar PDP

Sabuwar Rigima Za Ta Barke Tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike a Jam’iyyar PDP

  • Nyesom Wike yana goyon bayan Kingsley Chinda ya samu kujerar shugaban marasa rinjaye a Majalisa
  • Ana tunanin Atiku Abubakar su na da ‘dan takara dabam da na Gwamnan jihar Ribas mai barin kan mulki
  • ‘Dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 zai so Hon. Oluwole Oke ya maye gurbin Hon. Ndudi Elumelu

Abuja - Alamu na nuna rikicin ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP watau Atiku Abubakar da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike bai kare ba.

Wani rahoto da Leadership ta fitar ya bayyana cewa sabani na neman sake raba kan mutanen Atiku Abubakar da Nyesom Wike mai shirin barin-gado.

Ba komai ne yake kokarin haddasa wani danyen rikicin ba illa shugabancin majalisa.

Atiku
Atiku Abubakar da mutanen Oke a Majalisa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Kowane bangare na ‘yan siyasar ya na so ya samu dama a zaben shugabannin majalisar wakilan tarayya da za ayi a farkon watan Yuni mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan Haduwa da Tinubu a Kasar Waje, Kwankwaso da Abba Sun Dura Garin Legas

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da Wike ya ke kokarin ganin daga bangarensa aka samu sabon shugaban marasa rinjaye, wadanda ke tare da ‘dan takaran 2023 su na da ja.

Hon. Oluwole Oke v Hon. Kingsley Chinda

‘Dan majalisar Obokun/Oriade a Osun watau Hon. Oluwole Oke da Hon. Kingsley Chinda mai wakilatar Obio/Akpor ne su ke harin wannan kujera.

Idan rahoton ya zama gaskiya, Atiku Abubakar ya na goyon bayan Oluwole Oke ne yayin da shi kuma Gwamnan Ribas yake goyon bayan ‘dan jiharsa.

A majalisa ta tara, Wike ya yi bakin kokarinsa na ganin Chinda ya samu wannan matsayi amma bai yi nasara ba, Hon. Ndudi Elumelu ya doke shi.

Mai girma Gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa ne ya marawa ‘dan majalisarsa da ya fito daga mazabar Aniocha/Oshimili a zaben wancan lokaci.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Ganduje ya yi karin haske kan faifan muryarsa da ke yawo na sukar Tinubu

Alakar Atiku da Adeleke

A halin yanzu takarar Oke da kuma Chinda ta raba kan zababbun ‘yan majalisar PDP da duk sauran jam’iyyun hamayya fiye da 180 da za a rantsar.

Oke wanda tun 2015 yake majalisa ya fito ne daga Osun, nan ne kadai jihar da jam’iyyar PDP ta ke da mulki a Kudu maso yammacin Najeriya.

An yi wa doka karon tsaye - Kotu

Alkalin wata babban kotun tarayya da ke Kano ya ba Lauyan Alhassan Ado Doguwa gaskiya kan maganar garkame ‘dan majalisar tarayyar da aka yi.

Rahoto ya ce Mai shari’a Mohammed Yunusa ya ce kotun majistare ba ta da hurumin sauraron babban laifi irin wanda ake yi wa Doguwa na rike bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng