Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Ba 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa Muhimmiyar Shawara

Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Ba 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa Muhimmiyar Shawara

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya yi kira ga ƴan takarar shugabancin majalisa ta 10 da su mutunta tsarin karɓa-karɓa na APC da zaɓin Bola Tinubu
  • Gwamnan na PDP ya bayyana cewa wannan wata gagarumar hanya ce da za ta sanya gwamnati mai kamawa ta samu nasara domin Tinubu yana da na shi tsare-tsaren
  • Wike ya yi kira ga Tinubu da ya naɗa mutanen da suka cancanta a gwamnatinsa ba tare da la'akari da jam'iyyun da suka fito ba, ta yadda zai kama aiki ba ɓata lokaci

Kaduna, Kaduna - Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya buƙaci ƴan takarar da ke neman kujerun shugabancin majalisar dattawa da majalisar wakilai, da su mutunta matsayar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam'iyyar APC.

Wike ya bayyana cewa hakan zai taimakawa gwamnati mai jiran gado ta samu nasarar sauke alƙawuran da ta yi wa ƴan Najeriya a wajen yaƙin neman zaɓe, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babban Jigo a PDP, Bode George, Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a 29 Ga Mayu

Wike ya yi magana kan shugabancin majalisa ta 10
Gwamna Nyesom Wike tare da Bola Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ba Tinubu shawara da kada ya ɓata lokaci wajen naɗa ƙwararrun mutane cikin gwamnatinsa, da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Ya buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasan da ya zaɓi mutane waɗanda suka cancanta a cikin gwamnatinsa, ba tare da la'akari da daga jam'iyyun da suka fito ba, domin ya kama aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike, wanda babban jigo ne a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayar da wannan shawarar ne a birnin Kaduna, ranar Asabar, 20 ga watan Mayu, wajen ƙaddamar da wani littafi kan gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Gwamnan na jihar Rivers ya kuma yabawa gwamna El-Rufai bisa goyon bayan komawar mulki zuwa yankin Kudancin Najeriya domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Sama Da N200bn Muka Kashe a Ƙidayar Da Aka Ɗage, Cewar Shugaban Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa

Ga bidiyon nan ƙasa:

Har Yanzun Ina Cikin Tseren Kujerar Kakakin Majalisar - Wase

A wani rahoton na daban kuma, ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin majalisar wakilai ta 10, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram akan bakansa na neman kujerar.

Ahmed Idris Wase ya bayyana cewa bai janye takara ba, kuma baya da shirin janye takararsa saboda wani ɗan takara daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng