Sama Da N200bn Muka Kashe a Ƙidayar Da Aka Ɗage, Cewar Shugaban Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa

Sama Da N200bn Muka Kashe a Ƙidayar Da Aka Ɗage, Cewar Shugaban Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa

  • Nasir Isa Kwarra, Shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ya bayyana yadda ma'aikatarsa ta kashe kuɗi sama da N200bn a shirye-shirye
  • Ya bayyana cewa da farko an ware N800bn ne domin gudanar da aikin ƙidayar yawan gidaje da mutanen Najeriya
  • Ya kuma bayyana cewa a wajen aiki da wasu kayayyakin, da kuma horar da ma'aikata na wucin gadi ne aka kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe

Abuja - Shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya yi bayani kan yadda aka kashe N224bn da gwamnatin tarayya ta ware don aikin ƙidayar gidaje da yawan jama’a a 2023.

Isa Kwara ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, a yayin wani taro na karin kumallo da shugabannin kafafen watsa labarai kamar yadda jaridar Punch ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Nasiru Isa Kwarra
Shugaban Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa Ya Ce Sama Da N200bn Suka Kashe a Ƙidayar Da Aka Ɗage. Hoto: The Sun
Asali: UGC

N800bn aka ware da farko

Ya ce kuɗaɗen farko da aka ware domin gudanar da aikin sun kai Naira biliyan ɗari takwas (N800bn) amma daga bisani sai aka rage su bayan ɗagewar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Isa ya ce an kashe N224bn ɗin ne wajen shirye-shiryen gudanar da ƙidayar. An kashe su wajen abubuwan da suka haɗa da buga takardu, da horar da ma’aikata na wucin gadi, da dai sauransu.

Buhari ya ce Tinubu ne zai sanya lokacin da za a yi ƙidayar

Idan za ku iya tunawa, shugaban ƙasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya ɗage ƙidayar ne bayan ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki a ƙarshen watan Afrilu.

Ya ce gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu ce za ta yanke lokacin da za a gudanar da ƙidayar.

The Nation ta wallafa cewa, dalilin da hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta bayar na ɗage ƙidayar shine saboda a samu kwanciyar hankali a ƙasar gabanin aikin.

Kara karanta wannan

Ajali Ya Yi Kira: Wani Mutum Ya Mutu Bayan Faɗowa Daga Bishiyar Kwakwa a Abuja

Na yi nadamar goyawa Tambuwal baya

A wani labarin da muka wallafa a baya, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce ya yi nadamar goyawa Aminu Waziri Tambuwal baya a zaben majalisar wakilai ta bakwai a 2011.

Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja a wajen wani taro da jam'iyyar APC mai mulki ta kira kan batun zaben majalisar, wanda ya gudana a Otal din Transcorp Hilton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel