Batun Sukar Tinubu: Ganduje Ya Yi Karin Haske Kan Faifan Muryarsa Na Sirri da Ya Fita
- Gwamnatin Kano ta ce, ana son hada Ganduje da Tinubu da Masari fada gabanin rantsar da zababben shugaban kasa na Najeriya
- Wani faifan sauti ya fito, inda aka ji wasu bayanai daga bakin Ganduje, inda yake bayyana rashin jin dadinsa bisa kulla alakar Tinubu da Kwankwaso
- Akwai yiwuwar ‘yan jam’iyyun adawa su tashi da manyan kujeru a mulkin Tinubu, hasashe ya bayyana sunayen ‘yan siyasan
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta zargi ‘yan soshiyal midiya da jaridun yanar gizo da kokarin kirkirar labari daga wani kirkirarren faifan murya da aka yada na tattaunawar gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Kabiru Masari.
An yada wani faifan sautin da ke bayyana wata tattaunawar siyasa tsakanin jiga-jigan na APC biyu game da alakar Bola Ahmad Tinubu da abokin hamayyar Ganduje; Rabiu Musa Kwankwaso, rahoton Tribune Online.
Da take martani ga batun, gwamnatin jihar Kano ta bakin kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ta yi Allah wadai da masu kokarin kawo tsaiko ga siyasar APC.
Gwamnatin Kano ta yi bayani
A ranar Asabar, 20 Mayu, 2023 gwamnatin Kano ta fitar da sanarwa, inda tace faifan muryar da ke yawon sharri ne da kullaliya irinta ‘yan adawa da ake biya kudi don sauya maganar gwamnan zuwa baka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, gwamnatin ta zargi ‘yan adawa da kokarin dumama yanayin zaman lafiyar da jam’iyyar APC, Tinubu da Ganduje ke ciki a halin yanzu, Within Nigeria ta tattaro.
Kwamishinan ya ce, akwai alamun da ke nuna akwai wadanda ke adawa da dasawar Tinubu, Ganduje da Masari, don haka suka dauki aniyar rusa alakar.
Tinubu ya gane sharrin yan adawa
Malam Garba ya kuma bayyana cewa, tuni zababben shugaban kasa ya gano sirin da ake na bata tsakaninsa da Ganduje, kuma ba zai bari a samu tangardar alaka a tsakani ba.
Ganduje Ya Mayar Da Martani Ga Abba Gida-Gida, Ya Tona Babban Asirin Abinda Ya Faru Tun a Mulkin Kwankwaso
Daga nan, kwamishinan ya yi kira ga mambobin APC da su yi hakuri, kana su yi watsi da abin da ake yadawa a kafafen sada zumunta don jawo bakin jini tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.
A bangare guda, Tinubu na ta kokarin jawo 'yan jam'iyyun adawa kusa dashi, hasashe ya bayyana yiwuwar Kwankwaso ya samu bagas a mulkin Tinubu.
Asali: Legit.ng