‘Dan Majalisar APC Ya Tona Dalilin da Ya Sa Gbajabiamila Yake So Abbas Ya Gaje Shi
- Abubakar Nalaraba mai wakiltar Nasarawa a Majalisar Wakilai bai marawa Tajudeen Abbas baya
- ‘Dan majalisar ya na zargin Hon. Femi Gbajabiamila da kawo wanda zai iya juyawa a majalisar tarayya
- Hon. Nalaraba ya nuna sai inda karfinsu ya kare wajen yakar Abbas, su na tare da Hon. Muktar Betara
Abuja - Abubakar Nalaraba mai wakiltar yankin Nasarawa a majalisar wakilan tarayya, ya ce abokan aikinsa ba su tare da takarar Hon. Tajudeen Abbas.
Tajudeen Abbas shi ne wanda jam’iyyar APC ta tsaida a matsayin ‘dan takaran shugaban majalisa, The Cable ta ce wasu a majalisa su na ganin bai cancanta ba.
Abubakar Nalaraba ya ce ‘yan majalisa ba su goyon bayan Abbas ya zama shugaban majalisar wakilai, yake cewa kakaba masu shi aka yi da karfi da yaji kawai.
Nalaraba ya na zargin cewa shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi kutun-kutun, ya san yadda Hon. Abbas ya samu takara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun da mafi yawan ‘yan majalisa ba su goyon bayan shi wanda jam’iyya ta ayyana, Hon. Nalaraba ya ce idan ya yi nasara, to Gbajabiamila ne zai rika juya shi.
Korafin Abubakar Nalaraba yake yi
“Duk mun san ‘Dan takaran da suke so, Abbas Tajudeen ba sananne ba ne a majalisa. Ba mutum ba ne da yake da alaka mai kyau da sauran ‘yan majalisa.
Mu na fatan su (jam’iyyar APC) za su sake duba matakin da suka dauka, su kyale ayi zabe hankali kwance a ranar 13 ga watan Yuni da za a rantsar da majalisa.
Lamarin Abbas Tajudeen daga wajen Femi Gbajabiamila ya fito, shi kadai ya yi duk wani kutun-kutun ba tare da ya tuntubi sauran masu ruwa da tsaki ba.
Duba abin da ya faru. Kun fito da shugabannin majalisa biyu daga bangare guda. Ina aka baro Arewa ta tsakiya da ta ba APC kuri’u na biyu a yawa a zabe?
- Abubakar Nalaraba
An mai da Arewa maso Gabas saniyar ware
Vanguard ta rahoto ‘dan majalisar ya ce an yi watsi da yankin Arewa maso gabas duk da kuri'un da suka ba APC alhali Atiku Abubakar ya na takara.
Honarabul Nalaraba ya nuna ba za su goyi bayan mutum daya ya juya ‘yan majalisa 360 ba, yake cewa a tarihi babu shugaban majalisa da ya kakaba yaronsa.
A bayaninsa, an fahimci ‘dan majalisar yana cikin magoya bayan Hon. Mukhtar Aliyu Betara.
Siyasar Bola Tinubu
Rahoto ya zo cewa Bola Tinubu ya yi wa Rabiu Musa Kwankwaso tayin kujerun Ministoci a Gwamnatinsa, da alama zai jawo 'dan takaran na NNPP.
Zababben shugaban kasar ya sa labule da tsohon Gwamnan, ana tunanin tattaunawarsa da Kwankwaso a Faransa ta shafi har da takarar majalisa.
Asali: Legit.ng