Ganawar Tinubu Da Kwankwaso Ba Ta Yi Wa 'Yan APC Dadi Ba, Sun Ja Kunnen Zababben Shugaban Kasar
- Na kusa da shugaba Buhari kuma babban jigo a jam'iyyar APC a jihar, Kano ya fusata da ganin Tinubu na janyo Kwankwaso a jikinsa
- Dan Bilki Kwamanda gargaɗi Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ba Kwankwaso wani muƙami a gwamnatinsa
- Jigon na APC ya yi barazanar cewa idan Tinubu ya yi kunnen ƙashi, to tabbas za su sanya ƙafar wando ɗaya da shi
Jihar Kano - Babban jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, kuma na kusa da shugaba Buhari, Dan Bilki Kwamanda, ya ja kunnen zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Dan Bilki Kwamanda ya buƙaci Tinubu da ya bi a hankali wajen ƙoƙarin ƙulla wata alaƙar siyasa da Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar New Nigeria People Party (NNPP).
Jaridar Tribune ta kawo rahoto Dan Bilki na cewa yin hakan ba ƙaramin haɗari ba ne a siyasance ga jam'iyyar APC.
Da ya ke magana da manema labarai a birnin Kano, jagoran na APC ya yi watsi da batun Tinubu ya ba Kwankwaso wani muƙami ko da kuwa na ɗan aike ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan Bilki ya aike da muhimmin gargaɗi ga Tinubu
Dan Bilki ya kuma isar da wani muhimmin gargaɗin cewa, idan Tinubu ya yi ƙunnen ƙashi da kiraye-kirayen da suke masa, ya naɗa Kwankwaso wani muƙami, tabbas za su hargitsa jam'iyyar APC a Arewacin Najeriya, sannan su janye goyon bayansu gare shi.
Danbilki Kwamanda ya bayyana cewa magoya bayan Tinubu a Arewacin Najeriya, ba za su yi maraba da wata haɗaka ba tsakanin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da Kwankwaso ba.
Ya bayyana cewa wannan haɗakar za a yi mata kallon cin amanar magoya bayan Tinubu ne, a Arewacin Najeriya wanda hakan zai sanya su janye duk wani goyon bayan da suke ba shi.
Kwankwaso Ya Duro Najeriya, Ana Jiran Ya Fadi Yadda Suka Yi da Tinubu a Faransa
A wani rahoto a baya, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabiu Muss Kwankwaso, ya iso gida Najeriya daga ƙasar waje.
Dawowar jagoran na NNPP wanda ya sanya labule da Tinubu a ƙasara Faransa, ya sanya ana ta hanƙoron jin yadda tattaunawar su ta kaya.
Asali: Legit.ng