NNPP Ba ta da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu, Buba Galadima

NNPP Ba ta da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu, Buba Galadima

  • Babban jigon NNPP, Buba Galadima, ya ce jam'iyyar ta ƙauracewa kai kara Kotun zabe ne saboda rashin isassun kuɗi
  • Ya ce duk wanda ke shirin zuwa Kotu kalubalantar zabe, akalla yana buƙatar ware kudi naira biliyan N5bn
  • Manyan jam'iyyun adawa PDP da Labour Party sun kai karar kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu

Jigon jam'iyyar NNPP kuma tsohon makusancin shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya bayyana ainihin abinda ya hana jam'iyyarsu kalubalantar nasarar Bola Tinubu a Kotu.

Galadima ya ce jam'iyyar NNPP mai kayan marmari da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso, sun gaza kai ƙara Kotu ne saboda rashin kuɗi.

Buba Galadima.
NNPP Ba ta da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu a Ƙotu, Buba Galadima Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Babban jigon siyasar ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da kafar watsa labarai Arise TV kan muhimman batutuwan da suka mamaye siyasar Najeriya a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Halascin Takarar Zababɓen Gwamna da Wasu 'Yan Takara a Jihohin Kano da Abiya

Yayin da yake martani kan ko meyasa NNPP ba ta kalubalanci nasarar Bola Tinubu a Kotu ba kamar yadda jam'iyyar PDP, LP da sauran jam'iyyu suka yi, Galadima ya ce ba su da isassun kuɗi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Share tantama daga bakin jigon NNPP

Daily Trust ta rahoto Jigon NNPP na cewa:

"Da farko bari na fara share wata tantama, Jam'iyyar PDP ce ta kore mu ni da Kwankwaso, saboda haka ba mu shiga takara domin hana su lashe zaɓe ba."
"Sannan batun zuwa Kotu, kowa ya san cewa ana bukatar kashe makudan kuɗi kuma bamu da su. Ɗan kokarin da aka ga mun taɓuka saboda cancantar mu ne ba girman aljihunmu ba."
"Duk mutumin da ya zabi garzaya wa Kotu ya ƙalubalanci zaɓe, dole wannan mutumi ya ware zunzurutun kuɗi aƙalla naira biliyan N5bn, kuma a zahirin gaskiya ba mu da su."

Kara karanta wannan

Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023

Bugu da ƙari, Galadima ya ce NNPP ce ke ɗa gamsassun hujjoji amma rashin kuɗi ya sa ta hakura da batun zuwa Kotun sauraron zaɓen shugaban ƙasa.

"Kana da Yancin Faɗar Ra'ayinka," FG Ta Maida Martani Ga Matawalle

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari ta maida martani ga kalaman Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, wanda ya nemi EFCC ta fara kwamuso ministoci.

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce gwamnan yana da yancin faɗin duk abinda ke ransa, wannan ra'ayinsa ne.

Matawalle ya nemi shugaban EFCC ya sa kafar wando ɗaya da Ministoci masu barin gado kan zargin almundahana maimakon ya fara yi wa gwamnoni bi ta da ƙulli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262