Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na so da zarar ya shiga ofis, ya shiga aiki babu kama hannun yaro
  • Nan da kwanaki 11 za a rantsar da sabon shugaban kasa da zai gaji Muhammadu Buhari a Aso Rock
  • Tinubu yana so kafin tafiya tayi nisa, ya sanar da mutanen da za su zama Ministocin gwamnatinsa

Abuja - Ana samun karin bayanai a game da shirye-shiryen da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ke yi na karbar shugabancin Najeriya a karshen watan Mayu.

Wani rahoto da Nigerian Tribune ta kadaita da shi ya nuna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shirya soma aiki gadan-gadan da zarar an rantsar da shi a mulki.

Wata majiya ta ce zababben shugaban na Najeriya ya fahimci akwai nauyi da burin jama’a a kan shi, saboda haka yake so ya nada mukarrabansa tun wuri.

Kara karanta wannan

Jerin Taro, Wasanni da Shagulgulan Mika Mulki 12 da Za a Shirya na Tsawon Kwana 7

Bola Tinubu
Bola Tinubu rike da takarda Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Idan labarin da mu ke samu ya tabbata, a ranar 29 ga watan Mayu za a sanar da wadanda za su zama Ministocin tarayya da ‘yan majalisar tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a tafi da Ganduje da Wike

Wani na-kusa da shugaban mai jiran-gado ya shaidawa jaridar Abdulahi Ganduje, Nyesom Wike, da Kayode Fayemi sun fito a wadanda za su rike kujeru.

Ana tunanin bada mukamai ga tsohon shugaban NUC, Farfesa Peter Okebukola da kuma jagoran APC, Mallam Nuhu Ribadu wanda shi ya fara rike EFCC.

Majiyar ta ce akwai Aisha Benani, Farfesa Yemi Oke, Babatunde Ogala, Wale Edun, Mofe Boyo, Yewande Sadiku, Ayo Abina, Iyin Aboyeji da Uju Ohanenye.

Tsakanin Ganduje, Wike, Ribadu, Fayemi da Okebukola za a samu Ministan harkar gona, na cikin gida, harkar ‘yan sanda, da na harkar waje da Ministan ilmi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Duro Najeriya, Ana Jiran Ya Fadi Yadda Suka Yi da Tinubu a Faransa

Watakila Ogala ya zama AGF, sai Edun da Ayo Abina su rike kujerar Ministan tattalin arziki. Akwai yiwuwar Tinubu ya dauko wadanda ba ‘ya ‘yan APC ba.

Wadanda ake tunanin ba Ministocin wuta da masana’antu su ne Aisha Binani da Yewande Sadiku. Akwai yiwuwar Mofe Boyo ya zama sabon Ministan man fetur.

Kafin a je ko ina ake sa rai za a sanar da wadanda za su bada shawara kan tattalin arziki da jami’an da za su rike shugabancin hukumomin da ke tatso kudin shiga.

Za a binciki Ministoci?

Za a tono jan aiki domin labari ya zo cewa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya fadawa Hukumar EFCC ta binciki Ministoci da jami’an Aso Rock.

Gwamnan Zamfara mai barin-gado ya ce dole EFCC ta binciki har da Ministocin da za su bar mulki, a bincikensu duk ya tsaya a kan gwamnatocin jihohi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng