Gwamnan Jihar Benue Zai Mika Mulki Kafin 29 Ga Watan Mayu, Ya Bayyana Dalilansa

Gwamnan Jihar Benue Zai Mika Mulki Kafin 29 Ga Watan Mayu, Ya Bayyana Dalilansa

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana aniyarsa ta miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar kafin ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Ortom ya kuma bayyana cewa ba zai bar jihar ba bayan ya miƙa mulki ga Hyacinth Alia, ɗan takarar APC da ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamnan ya kuma karrama Manjo Gideon Orkar, wanda aka halaka saboda hannun da ya ke da shi a ƙoƙarin yi wa Janar Ibrahim Babangida juyin mulki a shekarar 1992

Makurdi, Benue - Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa zai miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar a ranar 28 ga watan Mayu, kwana guda kafin ranar da kundin tsarin mulki ya tanada domin miƙa mulki.

A cewar rahoton Tribune, gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar zartaswar jihar, wanda aka gudanar a birnin Makurdi, babban birnin jihar a ranar Talata, 16 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Gwamna Ortom ya bayyana ranar da zai mika mulki
Gwamna Samuel Ortom zai mika mulkin kafin ranar 29 ga watan Mayu Hoto: PDP Update
Asali: Twitter

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba zai bar jihar ba, bayan ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Rev. Fr. Hyacinth Alia, cewar rahoton Vanguard.

Alia, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya lallasa ɗan takarar Ortom da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen gwamnan jihar na ranar 19 ga watan Maris, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan watsa labarai, al'adu da yawon buɗe ido na jihar, Michael Inalegwu, shine ya bayyana aniyar gwamnan ta ƙin barin jihar, jim kaɗan bayan an kammala taron majalisar zartaswar jihar ranar Talata.

Ortom ya karrama tsohon soja

Gwamna Ortom ya tuna da wani babban ƙusa a jihar, inda ya karrama Manjo Gideon Orkar, ta hanyar sanya wa wata hanya mai tsawon kilomita 9 sunansa.

Manjo Orkar sananne saboda hannun da ya ke da shi a ƙokarin yi wa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, juyin mulki a shekarar 1992, an same shi da laifi inda daga baya aka halaka shi.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnoni Masu Barin Gado Da Za Su Bar Magadansu Da Biyan Bashin Albashin Ma'aikata

Gwamnatin Ortom tace ta ɗauki wannan matakin ne saboda abinda Manjo Orkar, ya tsaya domin sa.

Jam'iyyar APC Ta Soke Dakatarwar Da Aka Yi Wa Jiga-Jiganta a Benue

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa wasu jiga-jiganta a jihar Benue.

Uwar jam'iyyar ta ƙasa ce dai ta soke dakatarwar da aka yi wa sanata Barnabas Gemade, Farfesa Terhemha Shija, da wasu mutum biyar a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel